Tsohuwar Ministar Buhari Ta Faɗi Waɗanda Suka Yi Kutun Kutun Ta Rasa Kujerarta
- Tsohuwar ministar kuɗi, Kemi Adeosun, ta yi magana game da rasa kujerarta da ta yi a mulkin Muhammadu Buhari
- Adeosun ta ce manyan maƙiyanta a gwamnatin Buhari sun yi amfani da batun shaidar NYSC wajen tilasta mata murabus
- Ta bayyana cewa ta sanar da marigayi Buhari kafin murabus, tana mai cewa ba za ta iya ci gaba da aiki tana ƙarar gwamnatin tarayya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohuwar ministar kudi, Kemi Adeosun ta danganta murabus ɗinta da wasu makiyanta a gwamnati.
Adeosun ta danganta haka da kutun-kutun din wasu manyan maƙiya masu ƙarfi a cikin gwamnati.

Source: Twitter
Tsohuwar ministar ta bayyana haka ne a wata hira da ta yi a gidan talabijin na Channels a yau Alhamis 1 ga watan Janairun 2025.
Takardun bogi ya tilasta minista murabus
Wannan ba shi ne karon farko ba da minista a Najeriya ke murabus kan takardun bogi wanda aka yi ta maganganu a kai.
A kwanakin baya, Ministan kimiyya, kirkire-kirkire da fasaha na Najeriya, Geoffrey Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukamin da yake kai.
Rahotanni sun bayyana cewa Geoffrey Uche Nnaji ya ajiye aiki ne bayan zarginsa da ake yi da yin jabun takardu guda biyu.
Yayin da Shugaba Bola Tinubu ya karɓi murabus ɗinsa, Nnaji ya ce yana fuskantar batanci sosai daga abokan adawar siyasa.
Zargin da Adeosun ta yi kan barin kujerarta
Adeosun ta ce batun zargin shaidar NYSC ya zama dama ga waɗanda ke son kawar da ita daga mukami.
Ta bayyana cewa kafin ta yi murabus, ta gana da Shugaba Buhari, inda ta sanar da shi shirin kai ƙara kotu domin wanke sunanta daga zarge-zargen.
A cewarta, ba zai yiwu ta ci gaba da zama minista ba yayin da take ƙarar gwamnatin tarayya, tana mai cewa hakan ba daidai ba ne a siyasa.
Adeosun ta ce Shugaba Buhari ya goyi bayan matakinta, yana mai cewa barin suna mai kyau yana da amfani kuma bai kamata a lalata shi ba.

Source: Depositphotos
Hukuncin kotu kan dambarwar Kemi Adeosun
A shekarar 2021, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci cewa Adeosun ba za a hukunta ta ba saboda rashin gabatar da shaidar NYSC.
Alkalin kotun, Taiwo Taiwo, ya ce babu wani doka da ta tilasta Adeosun gabatar da shaidar NYSC domin rike mukamin gwamnati a Najeriya.
Sai dai kotun ba ta yi tsokaci kai tsaye kan zargin cewa shaidar NYSC da aka ambata an yi mata jabun ba.
Dalilin da ya sa Nnaji ya yi murabus
Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa bayan an taso shi a gaba kan zargin aikata ba daidai ba.
Uche Nnaji ya sauka daga mukaminsa ne bayan zargin da aka yi masa na yin amfani da takardun bogi.
Majiyoyi sun bayyana ainihin dalilin da ya sa tsohon ministan ya hakura da mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng

