Tonon silili: An gano yadda Ministar Kudi tayi amfani da shaidar tsallake NYSC ta bogi
Wani rahoto da Premium Times ta wallafa a yau ya tabbatar da cewa Ministar Kudi, Kemi Adeosun ba ta halarci shirin yiwa kasa hidima (NYSC) wanda ya zama wajibi ga duk dan Najeriya da ya kammala karatun digiri kuma bai wuce shekaru 30 ba.
Baya ga kasancewa dole ni mutum ya bayyana takardan kammala hidiman kasar kafin a dauke shi aikin gwamnati ko kuma na kamfani a Najeriya, akwai hukunci da doka ta tanada ga duk wanda ya tsere daga hidiman kasar ko kuma ya buga takardan kammala hidimar kasar ta bogi.
Sashi na 13 a dokar NYSC ta tanadar da hukuncin zaman gidan yari na watanni 12 da tarar N2,000 ko kuma a hada ma mutum dukka biyun.
Sashi na 13(3) shi kuma ya tanadar da hukuncin gidan yari na shekaru uku ko kuma zabin biyan tara ta N5,000 ga duk wanda ya saba dokar kamar yadda Ministan Kudi Kemi Adeosun tayi.
DUBA WANNAN: Dokar ta baci: 'Yan PDP zasu garzaya kotu don hana Buhari kwace kadarorinsu
Takardun karatun Mrs Adeosun wanda Premium Times ta binciko ya nuna cewa Ministan tayi ikirarin cewa an bata sheddan kammala hidimar kasar irin wadda ake bawa mutanen da suka wuce shekaru 30 a yayin da suka kammala jami'a a watan Satumban 2009.
Bayan ta kammala karatun ta, Adeosun ta yi ayyuka a kamfanoni da dama a kasar Ingila sannan daga baya ta dawo gida Najeriya, ta rike mukamin Kwamishiniyar Kudi a jihar Ogun.
Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa a lokacin da shugaba Buhari ya aike da sunan Adeosun ga majalisar tarayya don a tantance ta, 'yan majalisar sun ankare da wannan matsalar amma su kayi gum da bakinsu.
A halin yanzu, majalisar na amfani da Ministan wajen samun haramtattun kudi daga lalitar gwamnatin tarayya wanda ya hada da N10 biliyan da ta bawa majalisar cikin kwanakin da suka wuce domin su biya kamfanonin da suka yi musu odar motocci daga kasashen waje.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng