Kungiyar NLC Ta Fara Gwagwarayar Neman Karin Albashi ana Shiga 2026

Kungiyar NLC Ta Fara Gwagwarayar Neman Karin Albashi ana Shiga 2026

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta ce darajar albashin ma’aikata ya ragu sakamakon tsadar rayuwa da hauhawar farashi, tana mai bukatar a waiwaici albashi
  • Kungiyar ta bayyana 2026 a matsayin shekara mai muhimmanci wajen matsa lamba da tattaunawa da gwamnati kan manufofin da aka aka kawo a kasar
  • NLC ta kuma yi gargadi cewa za ta ci gaba da hada kai da shirya ma’aikata a dukkan matakan gwamnati domin tabbatar da gaskiya da adalci a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar Kwadagon Najeriya, NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta duba albashin ma’aikata a fadin kasar nan.

Ta yi magana tana mai bayyana cewa tsadar rayuwa da hauhawar farashi sun rage darajar kudin shigan ma’aikata yayin da aka shiga shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawo shirin tallafi na 2026, talakawa miliyan 10 za su amfana

Shugaban NLC da Bola Tinubu
Bola Tinubu da shugaban NLC, Joy Ajaero. Hoto: Bayo Onanuga|NLC HQ
Source: UGC

A sakon sabuwar shekara da ta aike ga ma’aikata da al’ummar Najeriya baki daya, NLC ta ce shekarar 2025 ta kara tsananta wahala ga talakawa, amma hakan bai sa kungiyar ta sassauta kudurinta na neman adalci da daidaito ba.

Sakon, wanda shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa 2026 za ta zama shekara cike da muhimmin shiri tare da kara hada kan ma’aikata a duk fadin kasar nan.

NLC ta dage kan bukatar duba albashi

Kungiyar ta bayyana cewa babban bukatarta ita ce a yi cikakken dubi kan albashin ma’aikata domin ya dace da halin tattalin arziki da ake ciki a yanzu.

Kungiyar NLC ta ce hauhawar farashi ya kai matakin da albashin da ake biya a yanzu ba zai iya biyan bukatun rayuwa ba a kasar nan.

Shugaban 'yan kwadagon Najeriya
Shugaban 'yan kwadago, Joy Ajaero. Hoto: NLC HQ
Source: Facebook

A cewar kungiyar, wannan yanayi ya sabawa alkawarin biyan albashin da zai ba da damar daukar dawainiyar rayuwa, ba wai kawai taimakawa mutum ya samu na kashewa ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ana zargin uwargida ta hallaka mijinta saboda ya yi mata kishiya

Ta jaddada cewa za ta yi amfani da duk hanyoyin halal da ke hannunta domin ganin an inganta albashi da walwalar ma’aikata a 2026.

Alakar NLC da gwamnatoci a Najeriya

NLC ta bayyana cewa a shirye take ta shiga tattaunawa mai zurfi da gwamnatin tarayya, bayan alkawarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yin hulda mai ma’ana da amana da kungiyoyin kwadago.

Kungiyar ta ce irin wadannan alkawura ba su zo da sauki ba, sai da matsin lamba da tsayin daka da ma’aikata suka nuna a baya.

Ta kara da cewa za ta goyi bayan gwamnatoci ko ‘yan siyasa ne kawai idan manufofinsu sun bayyana a fili cewa suna tare da jama’a.

Tinubu ya kawo shirin tallafi a 2026

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya jawabi na musamman game da sabuwar shekarar 2026.

Bola Tinubu ya sanar da kawo shiri na musamman da zai mayar da hankali kan tallafawa 'yan Najeriya miliyan 100 a shekarar da muka shiga.

Sanarwar shugaban kasar ta kara da cewa za a zakulo mutum 1,000 a kowace mazaba a dukkan sassan Najeriya domin su ci gajiyar shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng