Tinubu Ya Kawo Shirin Tallafi na 2026, Talakawa Miliyan 10 za Su Amfana
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirin tallafa wa a kalla mutum 1,000 a kowace mazaba cikin mazabu 8,809 na kasar nan a shekarar 2026
- Shirin, wanda aka sanya masa suna Renewed Hope Ward Development Programme, na da nufin shigar da fiye da ’yan Najeriya miliyan 10 harkokin kudi
- Tinubu ya ce nasarorin tattalin arziki da aka samu a 2025, ciki har da raguwar hauhawar farashi da karuwar GDP, sun nuna cewa ya samu nasara sosai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa shekarar 2026 za ta kasance sabon babi na karuwar tattalin arziki mai karfi da za ta haifar da canje-canje masu tabbas a rayuwar al’ummar Najeriya.
Tinubu ya fadi hakan ne a sakon taya murnar sabuwar shekara da ya aikewa ’yan kasa a ranar 1, Janairu, 2026, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki daga tushe.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da shugaban kasar ya yi ne a wani sako da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.
2026: Tinubu ya kawo shirin tallafi
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa shirin Renewed Hope Ward Development Programme zai kasance ginshikin dabarun gwamnatinsa na shigar da ’yan kasa cikin harkokin samar da kudi.
Ya ce shirin zai kai ga tallafa wa a kalla mutum 1,000 a kowace mazaba, wanda hakan zai kai ga fiye da mutane miliyan 10 a fadin kasa.
Ya kara da cewa za a aiwatar da shirin ne ta fannoni daban-daban kamar noma, kasuwanci, sarrafa abinci da hakar ma’adinai, domin farfado da tattalin arzikin yankuna da dama tare da samar da damar dogaro da kai ga matasa da mata.
Tinubu ya ce ya samu nasara a 2025
Tinubu ya ce shekarar 2025 ta kasance shekara mai muhimmanci wajen sake fasalin harkokin kudi, inda gwamnatinsa ta aiwatar da sauye-sauye. Ya ce duk da kalubalen tattalin arzikin duniya, Najeriya ta samu ci gaba mai yawa.
A cewarsa, GDP ya samu karuwa a baki dayan shekarar 2025, inda ake sa ran karuwar darajar tattali za ta wuce kashi 4 cikin 100.
Leadership ta wallafa cewa ya ce hauhawar farashi ya ragu a hankali har ya sauka kasa da kashi 15 cikin 100, daidai da burin da gwamnati ta sanya.

Source: Facebook
Shugaban ya ce kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta fi takwarorinta a 2025, inda ta samu karin kaso 48.12 cikin 100. Ya kara da cewa asusun wajen kasar ya kai dala biliyan 45.4 zuwa 29, Disamba, 2025, lamarin da ya karfafa darajar Naira.
A bangaren tsaro, Shugaban ya ce an dauki matakai masu tsauri kan kungiyoyin ta’addanci a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, tare da hadin gwiwar kasashen waje.
An bukaci Ibo su goyi bayan Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa ministan ayyuka na kasa, David Umahi ya yaba da matakan da shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka a Kudu maso Gabas.
Umahi ya bayyana cewa Tinubu ya kulla alaka mai kyau da yankin, inda ya warware dukkkan korafin da suke da shi da ya sanya su neman kafa Biyafara.
Legit Hausa ta rahoto cewa ministan ya yi kira ga 'yan kabilar Ibo da su shirya ba Bola Tinubu cikakken goyon baya a zaben 2027.
Asali: Legit.ng

