Duniya Labari: Sanata Mai Ci a Najeriya Ya Rasu a Indiya yayin Jinya
- Sanata Godiya Akwashiki na jihar Nasarawa ya rasu a kasar Indiya yana da shekaru 52 bayan fama da doguwar rashin lafiya
- Marigayin ya kafa tarihin zama sanata na farko daga shiyyar Nasarawa ta Arewa da ya samu nasarar lashe zabe sau biyu a jere
- Akwashiki ya kasance jajirtaccen dan siyasa wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban majalisar dokokin Nasarawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Indiya - Legit Hausa ta samu labarin rasuwar Sanata Godiya Akwashiki, sanatan da yake wakiltar shiyyar Nasarawa ta Arewa a majalisar dattijai ta kasa.
Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, sanatan ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar Laraba, 31 ga watan Disamba, 2025.

Source: Twitter
Sanatan Nasarawa ya rasu a asibitin Indiya
Akwashiki wanda ya ke da shekara 52 a duniya, ya rasu ne a wani asibiti da ke ƙasar Indiya, inda ya shafe lokaci yana jinya, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan
Dalibai za su mamaye Aso Rock, an sanya ranar zanga zangar adawa da harajin Tinubu
Marigayi Akwashiki ya fara fuskantar matsalolin lafiya ne tun bayan sake zaɓen sa a shekarar 2023, inda ya yi jinya a asibitoci daban-daban a Najeriya, Burtaniya, da kuma Indiya.
Sanatan, wanda mamba ne a jam’iyyar SDP, ya kafa tarihi a matsayin sanata ɗaya tilo daga shiyyar Nasarawa ta Arewa da ya taba samun nasarar komawa majalisar sau biyu a jere tun bayan ƙirƙirar jihar.
Takaitaccen tarihin sanatan da ya rasu
Kafin ya kai ga matakin majalisar ɗattijai, Godiya Akwashiki ya yi fice a majalisar dokokin jihar Nasarawa, inda ya riƙe muƙamin shugaban masu rinjaye.
Sanata Godiya Akwashiki, ya kuma taki nasarar siyasa, inda ya zama mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa.
An haife shi a ranar 3 ga watan Agusta, 1973, a garin Angba Iggah da ke ƙaramar hukumar Nassarawa Eggon.
Rahoto ya tabbatar da cewa marigayi Sanata Akwashiki ya kasance ɗan siyasa mai kyakkyawar alaƙa da talakawan mazabar Nasarawa ta Arewa.

Source: Facebook
An yi alhinin rasuwar sanatan Nasaarawa
A lokacin da yake majalisar ɗattijai, ya fi mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa, ilimi, tallafawa matasa, da kuma samar da ababen more rayuwa a shiyyarsa.
Abokan aikinsa da shugabannin al'umma sun bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga jihar Nasarawa da kuma siyasar ƙasa baki ɗaya.
Har yanzu iyalansa ba su fitar da sanarwar ranar da za a gudanar da jana'izarsa ba, yayin da Legit Hausa za ta ci gaba da kawo maku karin rahotanni a kan hakan.
Sanata Okey Ezea ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Najeriya ta yi babban rashi bayan da aka sanar da mutuwar sanata mai ci wanda ya bar duniya bayan fama da jinya.
An tabbatar da cewa Sanata Okey Ezea, wanda yake wakiltar Enugu ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya rasu a Birtaniya yayin da yake karɓar magani.
Mutanen Enugu ta Arewa da magoya baya sun bayyana alhini, saboda sanatan yana daga cikin fitattun jiga-jigan da suka tsaya da jam’iyyar LP.
Asali: Legit.ng
