An Jefa Kwamishinan Bauchi a Gidan Yari, Ana Zarginsa da Daukar Nauyin Ta'addanci

An Jefa Kwamishinan Bauchi a Gidan Yari, Ana Zarginsa da Daukar Nauyin Ta'addanci

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da wani kwamishinan Bauchi kan zargin karkatar da dalar Amurka miliyan tara domin daukar nauyin ta'addanci
  • Ana zargin kwamishinan ya tura kudaden ga shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo, bayan ya canja kudaden gwamnatin Bauchi zuwa dala
  • Kotu tura kwamishinan da ake zargi zuwa gidan yari, tare da sanya lokacin da za a saurari bukatar ba da belinsa da na wasu mutane uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da kwamishinan kuɗi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Laraba.

EFCC ta gurfanar da Yakubu Adamu ne tare da wasu mutane uku, Balarabe Abdullahi Ilelah, Aminu Mohammed Bose, da Kabiru Yahaya Mohammed.

Kara karanta wannan

Kudin babura: EFCC ta gurfanar da jami'in gwamnati kan zargin handame N5.79bn

EFCC na zargin kwamishinan Bauchi, Yakubu Adamu ya dauki nauyin ayyukan ta'addanci.
Kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu a hanyar shiga kotu a Abuja. Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Zargin kwamishina da daukar nauyin ta'addanci

Hukumar ta tuhumar kwamishinan da mutanen uku ne kan zarge-zarge guda 10 da suka shafi kashe dalar Amurka miliyan 9.7 a wajen daukar nauyin ta’addanci, in ji rahoton The Cable.

Sai dai, waɗanda ake tuhumar sun bayyana cewa ba su aikata dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masu ba a gaban Mai shari’a Emeka Nwite.

A cewar EFCC, kwamishinan da sauran mutanen sun haɗa baki wajen samar da tsabar kuɗi har dalar Amurka miliyan 2.3 domin amfanin shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo, da wasu mutane da ke da alaƙa da shi, bisa amincewar gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.

Hukumar ta bayyana cewa an yi amfani da waɗannan kuɗaɗen wajen tallafa wa ƙungiyar ta’addanci, wanda hakan ya saɓa wa dokar kariya da haramta ta’addanci ta shekarar 2022.

Takaddama kan ba da belin kwamishina

Lauyan waɗanda ake tuhuma, Gordy Uche (SAN), ya roƙi kotun da ta ba da su beli, inda ya bayyana cewa tuhume-tuhumen ba su nuna alaƙa ta zahiri tsakanin kuɗin da aka ce an kashe da ayyukan ta'addanci ba.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta cafke fiye da mutane 3,000 a Kano, kwamishina ya yi bayani

Ya kuma ƙara da cewa ci gaba da tsare kwamishinan kudi, Yakubu Adamu yana shafar biyan albashin ma'aikatan jihar Bauchi kusan 600,000.

Sai dai, lauyan EFCC, Samuel Chime, ya yi adawa da buƙatar belin, yana mai nuna girman laifin da kuma gaskiyar cewa Kwamishinan yana fuskantar wata shari'ar halatta kuɗin haram ta daban.

Kotu ta ba da umarnin a garkame kwamishinan kudi na jihar Bauchi a gidan yari
Harabar babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja. Hoto: @FederalHigh
Source: UGC

An jefa kwamishina a gidan yarin Kuje

Mai Shari’a Nwite ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Janairu, 2026, domin yanke shawara kan buƙatar belin wadanda ake kara.

Sannan ya bayar da umarnin a tsare waɗanda ake tuhumar a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.

EFCC ta kuma zargi Kwamishinan da ɓoye asalin kuɗaɗen gwamnatin jihar Bauchi ta hanyar amfani da ‘yan canji (BDC) domin mayar da su dalar Amurka don gudanar da ayyukan da suka saɓa wa doka.

Wani zargi da ake yi wa kwamishinan Bauchi

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, hukumar EFCC ta gurfanar da kwamishinan kudin jihar Bauchi, Yakubu Adamu bisa zargin ya karkatar da fiye da Naira biliyan biyar.

Kara karanta wannan

Fusatattun mutane sun farmaki ofishin hukumar NSCDC a Kano, an rasa rayuka

Ana zargin Yakubu Adamu ya karkatar da biliyoyin kudin da aka fitar don sayen wasu baburan gwamnati kafin Gwamna Bala Mohammed ya nada shi mukamin kwamishina.

Zarge-zargen da ake yi wa kwamishinan kudi da kamfanin sun shafi karkatarwa da halatta kuɗin haram da jimillarsu ta kai Naira biliyan 5.79, wadanda ya musanta su duka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com