An Fitar da Tambarin Aabuwar Hukumar Haraji ta Najeriya bayan Tinubu Ya Rusa FIRS
- An kaddamar da tambarin hukumar tattara haraji ta kasa watau NRS wacce za ta maye gurbin FIRS da gwamnatin tarayya ta rusa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya canza hukumar tattara haraji bayan rattaba hannu kan sababbin dokokin sauya fasalin harajin Najeriya
- Duk da sukar da ake yi, gwamnatin Najeriya ta dage cewa dokokin harajin za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabuwar hukumar tattara haraji ta kasa (NRS), wacce ta maye gurbin Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) da aka rushe.
Hukumar NRS ta fitar da sabon tambarinta, alamar da ke nuna cewa za ta fara aiki a hukumance bayan sababbin dokokin harajin Najeriya sun fara aiki a farkon 2026.

Source: Twitter
NRS ta fara aiki ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar kafa ta, wato Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Najeriya ta 2025 a watan Yunin 2025, kamar yadda Leadership ta rahoto.
An fitar da tambarin hukumar NRS
A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar, shugaban NRS na kasa, Zacch Adedeji, ya tabbatar da cewa an fitar da tambarin hukumar.
Adedeji, ya bayyana cewa sabon tambarin da sauran alamomin da aka kirkiro don shaidar NRS na nuni da wani muhimmin matakin da aka dauka da nufin kawo ci gaba a tsarin tafiyar da harkokin tara kuɗaɗen shiga na ƙasar nan.
Sanarwar ta ambato Adedeji yana cewa:
“Fitar da tambarin NRS na nuna yadda gwamnatin tarayya ta ƙuduri aniyar gina tsarin haraji da ya fi zama mai haɗin kai, inganci da mayar da hankali kan hidimar jama’a, kuma wanda ya dace da manufar sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya."
Ya jaddada cewa hukumar za ta fi maida hankali wajen tallafa masu biyan haraji da saukaka wa kowane dan Najeriya ta yadda kowa zai sauke hakkin da ke kansa cikin sauki.
Hukumar NRS za ta dora da ayyukan FIRS

Kara karanta wannan
Dalibai za su mamaye Aso Rock, an sanya ranar zanga zangar adawa da harajin Tinubu
Zacch Adedeji ya tabbatar wa yan Najeriya cewa hukumar NRS za ta dora daga wurin da tsohuwra hukumar haraji ta tsaya, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Ya ce NRS za ta ci gaba da jajircewa wajen kwatanta gaskiya, hadin gwiwa domin tattara kudaden shiga da za su amfani 'yan Najeriya.
“Hukumar Haraji ta Najeriya za ta ci gaba da jajircewa wajen kwatanta gaskiya, haɗin kai da jagoranci nagari.
"Wannan sabon tambari ba ƙarshen tafiya ba ce, sai dai ya kasance farkon ƙarfafa alaƙa tsakanin hukumar tara haraji da al’ummar Najeriya, alaƙar da aka gina bisa amana, fahimtar juna da ayyukan ci gaban da kowa zai amfana da ita,” in ji sanarwar.

Source: Twitter
NANS ta shirya zanga-zanga a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar daliban Najeriya ta ayyana ranar 14 ga Janairu a matsayinranar zanga-zangar adawa da dokokin harajin gwamnatin Bola Tinubu.
Shugaban ƙungiyar, Kwamared Olushola Oladoja, ya bayyana cewa ɗalibai ba su amince da matakin fara aiki da sababbin dokokin haraji daga 1 ga watan Janairu ba.
NANS ta bayyana cewa yunƙurin tilasta wa ‘yan Najeriya wannan doka ba tare da amincewar mafi yawancin jama’a ba ya saɓa wa tsarin dimuƙuradiyya.
Asali: Legit.ng
