Kotu Ta Yi Hukunci kan Bukatar Hana Aiwatar da Sababbin Dokokin Haraji

Kotu Ta Yi Hukunci kan Bukatar Hana Aiwatar da Sababbin Dokokin Haraji

  • Gwamnatin tarayya ta samu goyon baya kan shirin da take na fara aiwatar da sababbin dokokin haraji a watan Janairun 2026
  • Wata babbar kotu a Abuja ta ki amincewa da karar da aka shigar wadda ke neman dakatar da fara aiwatar da sababbin dokokin harajin
  • Alkalin kotun ya yi karin haske kan dalilin da ya sa ya ki amincewa da bukatar da masu shigar da kara suke nema

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babbar kotun Abuja ta yi hukunci kan karar da ke neman hana gwamnatin tarayya fara aiwatar da sababbin dokokin haraji.

Kotun ta ba gwamnatin tarayya, hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) da kuma majalisar tarayya damar ci gaba da aiwatar da sabon tsarin haraji da aka shirya fara amfani da shi daga 1 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Dokar haraji: Gaskiyar zance kan batun cire kudi daga asusun banki

Kotu ta yi hukunci kan sababbin dokokin haraji
Shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce kotun ta ba da damar ne bayan da ta yi watsi da karar da ke neman dakatar da aiwatar da sababbin dokokin harajin.

Kotu ta yi hukunci kan dokokin haraji

Hukuncin wanda mai shari’a Kawu Bello ya yanke a ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025 ya yi watsi da bukatar da kungiyar Incorporated Trustees of African Initiative for Abuse Public Trustees suka shigar.

Kungiyar ta nemi kotun ta hana gwamnati da hukumomin da abin ya shafa aiwatar da sababbin dokokin harajin, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.

Masu shigar da karar sun nemi kotu ta dakatar da aiwatar da dokokin, suna mai cewa akwai bambance-bambance da kura-kurai a cikin sababbin dokokin harajin tare da zargin cewa sun saba wa wasu tanade-tanaden doka.

Wane hukunci kotun ta yanke?

Sai dai mai shari’a Kawu Bello ya ce karar ba ta da tushe, domin ba a nuna yadda aiwatar da sababbin dokokin harajin zai haifar da babbar illa da ba za a iya gyarawa ba, ko kuma ya saba wa kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Bayan korafe korafe, Tinubu ya fadi lokacin fara aiwatar da dokar haraji

Kotun ta jaddada cewa batutuwan da suka shafi manufofin tattalin arziki da sauye-sauyen haraji suna cikin ikon gwamnati kamar yadda doka ta tanada.

"Da zarar an kafa doka, duk wani kuskure sai dai a gyara shi ta hanyar yin gyaran doka ko kuma umarnin kotu, idan akwai."
"Cece-kuce kan dokar haraji ba za su iya hana aiwatar da dokar da aka wallafa a hukumance ba, sai dai da sahihin umarnin kotu ko gyara fasalin doka.”

- Mai shari'a Kawu Bello

Kotu ta ba da damar aiwatar da sababbin dokokin haraji
Taswirar babban birnin tarayya Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kotun ta kuma bayyana cewa babu wata tangarda ta doka da ke hana aiwatar da sabon tsarin harajin, inda ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na da ’yancin fara cikakken aiwatarwa daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026.

Tinubu ya yi magana kan aiwatar da dokar haraji

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kan fara aiwatar da sababbin dokokin haraji.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa babu fashi kan fara aiwatar da sababbin dokokin a ranar 1 ga watan Janairun 2026.

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa bai ga wata babbar matsala da za ta sanya a dakatar da fara aiwatar da sababbin dokokin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng