Kallon Fim Ya Zama Fitina, An Caka Wa Matashi Wuka Har Lahira a Jihar Kano
- 'Yan sanda sun kama wani matashi, Mustapha Isma’il, dan shekara 25 bisa zargin caka wa abokinsa wuka har lahira a jihar Kano
- Wanda ake zargin ya bayyana cewa ya samu sabani da marigayin ne daga kallok fim a waya, wanda ta kai ga fada a tsakaninsu
- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Mustapha, inda ta ce za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Rundunar ’Yan Sanda reshen jihar Kano ta tabbatar da cafke wani matashi mai shekaru 25, Mustapha Isma’il, bisa zargin caka wa abokinsa, Halifa, wuka har lahira.
Rahoton binciken da 'yan sanda suka gudanar ya nuna cewa Mustapha ya halaka abokinsa ne sakamakon saɓani da ya shiga tsakaninsu kan kallon fim a wayar salula.

Source: Getty Images
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano (PPRO), CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Matashi ya caka wa abokinsa wuka a Kano
Ya kara da cewa lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Disamba, 2025, da misalin karfe 8:30 na dare, a unguwar Sheshe da ke cikin birnin Kano.
A cewar Abdullahi Kiyawa:
"Bayan mun samu kiran gaggawa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tura jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru.
"Jami'an 'yan sanda sun taras da wanda aka jikkata yana zubar jini, aka garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, amma daga bisani likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa.”
Ya ƙara da cewa an cafke wanda ake zargi nan take, sannan aka mika shi ga Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na rundunar 'yan sandan jihar Kano.
Abin da binciken 'yan sanda ya gano
Kakakin yna sandan ya ce binciken farko ya nuna cewa Mustapha Isma’il ya caka wa marigayin mai shekaru 24 wuka a cikinsa, bayan wata muhawara da ta ɓarke a tsakaninsu.
“Muna kan bincike, kuma wanda ake zargi ya amsa laifinsa, za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
“Muna kira ga jama’a, musamman matasa, da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa amfani da makamai duk lokacin da aka samu rashin fahimta,” in ji kakakin ’yan sandan.
Matashin ya fadi abin da ya hada su fada
Da yake ba da nasa labarin, wanda ake zargin ya ce saɓanin ya fara ne yayin da suke kallon fim a wayar hannu a gaban wani shago.
Ya ce suna cikin kallo, kwatsam Halifa ya fado cikinsu, wanda hakan ya sa ya gargaɗe shi cewa kada a lalata masa waya.

Source: Facebook
A cewarsa, daga nan ne rigima ta kaure, inda shi marigayin ya buge shi da wani abu har ya zubar da jini, kamar yadda Daily Post ta kawo.
“Ganin haka nima na shiga gida, na ɗauko wuka, sannan na caka masa. Daga baya na ji labarin cewa ya rasu.
"Ina matuƙar nadama kan abin da na aikata. Da na san hakan zai kai ga mutuwarsa, da ban fita daga gida a wannan ranar ba,” in ji shi.
Uwargida ta kashe mijinta a Kogi
A wani rahoton, mun kawo muku cewa ana zargin wata uwargida ta kashe mijinta, Abdul-Kadir Nagazi bayan ya kara aure kuma amarya ta haihu a jihar Kogi.
Majiyoyi sun bayyana cewa ma’auratan sun shafe kusan shekara tara da aure amma Allah bai nufa sun samu karuwa ta ɗa ba har dai da magidanci ya kara aure.
Dakarun 'yan sanda sun fara bincike kan lamarin da nufin kama matar da ta aikata wannan danyen aiki domin a yiwa yan uwansa adalci.
Asali: Legit.ng


