Jirgi Ya Yi Hatsari Dauke da Fasinjoji a Najeriya, fiye da Mutane 5 Sun Mutu
- Fasinjoji shida ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da aka ceto mutane hudu bayan wani jirgin ruwa ya yi hatsari a tsakiyar tekun Legas
- Hukumomin LASWA da NIWA sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon karon da jirgin ya yi da wani abu a cikin ruwa
- Jami'an aikin ceto na ci gaba da yin nutso cikin ruwa don tabbatar da cewa babu wani fasinja da ya rage a karkashin rua bayan hatsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Wani mummunan haɗarin jirgin ruwa ya afku a yankin Igbologun da ke jihar Legas a daren ranar Talata, inda fasinjoji shida suka mutu, yayin da aka ceto wasu mutum huɗu.
Wannan lamari marar dadi ya faru ne da misalin ƙarfe 8:35 na dare, a lokacin da jirgin fasinja na kamfanin "Savvy Marine" yake kan hanyarsa ta dawowa daga Ilashe Beach House.

Source: UGC
Mutane 6 sun mutu a hadarin jirgin ruwa
Wannan haɗari ya sake tayar da hankulan mazauna birnin Legas, musamman masu amfani da hanyoyin ruwa domin zirga-zirga a wannan lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara, in ji rahoton Punch.
Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas (LASWA) da takwararta ta tarayya (NIWA) sun fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa a ranar Laraba, inda suka tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar sanarwar da Wuraola Alake da Omowunmi Yussuff suka sanya wa hannu, hukumomin sun sami kiran gaggawa inda suka haɗa gwiwa da 'yan sandan ruwa domin gudanar da aikin ceto.
An garzaya da mutane huɗun da aka ceto zuwa asibiti mafi kusa domin karɓar magani, yayin da aka tsamo gawarwakin mutane shida a wurin da abin ya faru.
Abin da ya jawo hatsarin jirgin ruwan Legas
Binciken farko da masana suka gudanar ya nuna cewa jirgin ya yi karo ne da wani babban abu da ke maƙale a ƙarƙashin ruwa, wanda hakan ya janyo fashewar jirgin da kuma nutsewarsa cikin kankanin lokaci.
Hukumomin LASWA da NIWA sun miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da tabbatar wa jama'a cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin haɗarin.
Kazalika, sun gargaɗi masu tafiye-tafiye ta ruwa da su riƙa kiyaye dokokin tsaro, musamman dokar hana tafiyar dare wadda ta nuna cewa bai kama jirgi ya kasance a hanyar ruwa bayan faɗuwar rana ba.

Source: Original
Gargadin da aka sha yi wa masu jiragen ruwa
Wannan haɗari ya zo ne a daidai lokacin da hukumomin ruwa ke tsaka da ayyukan wayar da kai kan kiyaye haɗurra a lokacin hunturu da bukukuwa, inda ake samun ƙaruwar cinkoson fasinjoji.
Hukumomin sun buƙaci masu jiragen ruwa da su tabbatar da cewa dukkan fasinjoji sun sanya rigar kariya kuma su guji ɗora wa jiragen nauyin da ya fi ƙarfinsu.
A halin yanzu, ana ci gaba da aikin bincike a cikin tekun domin tabbatar da cewa babu wani fasinja da ya rage a ƙarƙashin ruwan, in ji rahoton shafin The Witness Nigeria.
Jirgi dauke da fasinjoji 571 ya kama da wuta
A wani labari, mun ruwaito cewa, jirgin fasinja KM Barcelona 5 dauke da akalla fasinjoji 571 ya kama da wuta yayin da yake tafiya a tsakiyar teku.
Jami’an ceto na kasar Indonesia sun tura jiragen ruwa da kwale-kwale don aikin agaji, inda suka yi nasarar ceto sama da mutane 650 daga cikin ruwan.
Jiragen ruwa a Indonesia na yawan fuskantar hadurra saboda cunkoso da rashin bin ka’idoji, kuma ana samu yawan mace-mace da asarar dukiyoyi.
Asali: Legit.ng

