'Ni ba Ɗan Ta'adda ba ne': Gwamna Bala Ya Fusata kan Alaƙanta Shi da Ta'addanci

'Ni ba Ɗan Ta'adda ba ne': Gwamna Bala Ya Fusata kan Alaƙanta Shi da Ta'addanci

  • Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulqadir Mohammed, ya yi karin haske game da zargin alakanta shi da harkar ta'addanci
  • Bala Mohammed ya musanta zargin ta’addanci, yana cewa bai da alaƙa da ‘yan ta’adda kuma bai taɓa goyon bayan aikata laifi ba
  • Ya bayyana fushinsa kan yadda EFCC ke tsare Kwamishinan Kuɗinsa, yana cewa ana amfani da hukumomi wajen muzgunawa ‘yan adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana karara cewa shi ba ɗan ta’adda ba ne.

Gwamnan wanda ya kusa gama wa'adinsa ya ce ba shi da wata alaƙa da ayyukan ta’addanci ko goyon bayan aikata laifuka a Najeriya.

Gwamna Bala ya musanta alaka da ta'addanci
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Gwamna Bala ya karyata zargin alaka da ta'addanci

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne yayin da yake karɓar Lambar Yabo ta Kwarewa a matsayin Jakadan Tsaro, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'An fara ruwan kudi': Gwamna ya biya ma'aikata albashin watan 13 bayan Kirsimeti

Bala Mohammed, wanda ya nuna bacin rai kan halin da Kwamishinan Kuɗinsa ke ciki a hannun Hukumar EFCC, ya ce abin da ke faruwa babban zalunci ne a kansa da gwamnatinsa.

A cewarsa:

“Ni jakadan tsaro ne. Ban san cewa abu ne mai girma haka ba sai da mai gabatarwa ya yi bayani. Ina karɓar wannan lambar yabo ne a madadin al’ummar Jihar Bauchi, domin a nan ne muka yi aiki tare muka samu wannan girmamawa.
“Abubuwan rayuwa cike suke da ruɗani da sabani. Na wayi gari ana cewa an zarge ni da ta’addanci a matsayina na gwamna.”

Ya ce duk da yana da kariya ta doka a matsayin gwamna, sunansa ya fito a kotu, yayin da Kwamishinansa ke tsare ba tare da ‘yanci ba.

Gwamna Bala ya soki salon mulkin Tinubu
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Gwamna Bala ya soki gwamnatin tarayya

Bala Mohammed ya bayyana cewa siyasa a Najeriya ta sauya salo, amma har yanzu akwai fatan samun ci gaba, cewar rahoton The Guardian.

Ya kuma koka da tsarin rabon albarkatu, yana cewa gwamnatin tarayya na karɓar kashi 51 cikin 100 na kuɗaɗe, alhali ba ta gina hanya ko samar da ruwa a Bauchi ba, har ma da tsaro gwamnatinsa ke biya.

Kara karanta wannan

Zulum ya nemi gafarar 'yan Borno, ya ja kunnen masu neman kujerarsa

Gwamnan ya ce:

“A ƙasar nan, idan ka yi aiki tuƙuru, za a kira ka wawa. Na yi shiru na dogon lokaci ne saboda zaman lafiya, amma ba matsoraci ba ne ni.”

Game da sabuwar dokar haraji, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sake dubawa, yana cewa ana aiwatar da dokar duk da kura-kuran da ke cikinta.

Bala Mohammed ya ce Bauchi na daga cikin jihohin Arewa mafi samun zaman lafiya, sakamakon haɗin kai da shugabanci na dimokiraɗiyya, inda jam’iyyu daban-daban ke zama lafiya.

Gwamnan Bauchi ya musanta rahoton barin PDP

Kun ji cewa Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa yana shirin fita daga PDP zuwa PRP.

Gwamna Bala ya kuma soki kalaman da PRP ta yi, yana mai cewa ba zai bari karya da kage su dauke masa hankali ba.

Gwamnatin Bauchi ta ce Gwamna Bala na taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin PDP kuma bai taba tunanin sauya sheka ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.