Sojojin Najeriya Sun Gwabza Fada da 'Yan Ta'adda a Borno, An Lalata Sansanoni 3

Sojojin Najeriya Sun Gwabza Fada da 'Yan Ta'adda a Borno, An Lalata Sansanoni 3

  • Sojojin Operation Hadin Kai sun hallaka dan ta'adda guda daya tare da tarwatsa sansanonin miyagun a cikin dajin Sambisa
  • Dakarun Najeriya sun yi nasarar kwace wani jirgi mai sarrafa kansa daga hannun 'yan ta'addan ISWAP a yankin Izge a Borno
  • Sojojin sun kuma yi nasarar kwace manyan makamai bayan sun fatattaki 'yan ta'addar da suke addabar mutane a ayyukan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Borno - Jami’an tsaro na rundunar Operation Hadin Kai sun samu gagarumar nasara a fafutukar yaƙi da ta’addanci a jihar Borno, inda suka hallaka ɗan ta’adda tare da lalata sansanoninsu da dama.

A ranar 28 ga watan Disamba, sojojin bataliya ta 151 tare da haɗin gwiwar dakarun sa-kai, suka yi kwanton ɓauna a yankin Ladantar da ke ƙaramar hukumar Bama.

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a Borno
Sojojin Najeriya da ke aikin kakkabe 'yan ta'adda a dajin Sambisa. Hoto: ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a Borno

Mai sharhi kan lamuran taro a Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya rahoto hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Nasarawa, an rasa rayukan bayin Allah

A yayin fafatawar da aka yi da tsakar dare, sojojin sun yi nasarar kashe ɗan ta’adda ɗaya yayin da sauran suka tsere da raunukan harsasai, ba tare da jami'an tsaro sun rasa kowa ba.

Bugu da ƙari, a ranar 30 ga watan Disamba, dakarun haɗin gwiwa na birgediya ta 21 da ta 26 sun kai farmaki na musamman mai suna Operation Desert Sanity V a cikin dajin Sambisa.

Sojojin sun kutsa har yankunan Ukuba, Parisu, Somalia Camp, da Njimiya, inda suka lalata sansanonin 'yan ta'addan.

Ko da yake 'yan ta'addan sun raba ƙafarsu kafin isar sojojin, dakarun sun yi nasarar ƙwace wasu manyan makamai da suka haɗa da babban kwankon gidan harsasai da gurneti guda ɗaya.

Sojoji sun kwace mataki mai sarrafa kansa

Hakazalika, sojojin da ke sansanin Izge sun yi nasarar ƙwace wani jirgi mai sarrafa kansa daga hannun mayakan ƙungiyar ISWAP a ranar 30 ga watan Disamba.

Jami'an tsaron sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan ne yayin da suke gudanar da sintiri a yankin Pridang na jihar Borno, in ji rahoton PR Nigeria, wata kafar labarai ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Yadda hare haren sojoji ke raunana 'yan bindiga, sun shiga bala'i a Zamfara

Ana zargin 'yan ta'addan sun fito ne da jirgin domin yin leƙen asiri kan ayyukan sojoji da mazauna yankin kafin su kai farmaki.

'Yan ta'adda na ci gaba da kwasar kashinsu a hannun sojojin Najeriya.
Taswirar jihar Borno da ke a Arewa maso Gabas inda sojoji ke kakkabe 'yan ta'adda a Sambisa. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji za su ci gaba da tumurmusar 'yan ta'adda

An rahoto cewa sojojin sun yi amfani da kwarewar yaki wajen fatattakar 'yan ta'addan, wanda hakan ya tilasta musu jefar da jirgin da dukkan kayan aikinsa suka tsere.

Wannan nasara ta nuna yadda sojoji suka ƙara kaimi wajen amfani da fasaha da bayanan sirri domin dakile dabarun 'yan ta'adda a Arewa maso Gabas.

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da matsa lamba a cikin dajin Sambisa da yankunan karkara har sai an kawar da ragowar ɓata-garin baki ɗaya.

Sojoji sun wargaza lissafin Boko Haram

A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta kai gagarumin farmaki kan sansanin ‘yan Boko Haram a yankin Arra, cikin dajin Sambisa.

Sanarwar da jami'in hulda da jama’a na rundunar, Ehimen Ejodame, ya fitar ta bayyana cewa bangaren Operation Hadin Kai ne ya kaddamar da farmakin bayan bincike.

An ce an kai wa sansanin farmaki wanda ya tarwatsa cibiyoyin sadarwa da gine-ginen da suke amfani da su wajen shirya hare-hare, tare da raunana karfin Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com