'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Nasarawa, an Rasa Rayukan Bayin Allah
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Lafia ta jihar Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya
- Tsagerun 'yan bindiga sun hallaka bayin Allah tare da raunata mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
- Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar aukuwar lamarin tare da tura karin jami'an tsaro zuwa yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - Wasu ’yan bindiga sun kai harin ta'addanci a kauyen Kunza, cikin gundumar Ashigye da ke karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa.
'Yan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025 inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce majiyoyi da dama, da suka nemi a sakaya sunansu, sun ce harin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na dare. da dama, da suka nemi a sakaya sunansu, sun ce harin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na dare.
'Yan bindiga sun yi aika-aika a Nasarawa
Kauyen Kunza na kan babbar hanyar Lafia–Shendam, kimanin kilomita 50 daga Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.
Sun danganta tashin hankalin da rikicin da ya dade yana gudana tsakanin Fulani makiyaya da al’ummar yankin, wanda a bara ya haddasa kashe-kashe a bangarorin biyu.
Majiyoyin sun kuma nuna wani lamari da ya faru a ranar Lahadi da ta gabata, inda ake zargin wasu sun yi wa Fulani Makiyaya biyu kwanton bauna a kusa da wata gada da ke yankin Akunza–Ashigye, inda aka ce daya daga cikinsu ya rasu.
An yi kira ga gwamnatin Nasarawa
Mutanen kabiliar Migili wadda da ta fi yawa a yankin, sun tabbatar da faruwar harin tare da yin Allah-wadai da shi.
Shugaban kungiyar matasan Migili, Sheh Oli Christopher, ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci kuma abin kyama, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Ya nuna damuwa kan ci gaba da tabarbarewar tsaro a yankin, yana mai cewa mutane musamman mata, yara da tsofaffi, na rayuwa cikin fargaba.
Christopher ya bukaci gwamnatin jihar da ta tura isassun jami’an tsaro zuwa yankunan da ke da hadari, tare da tabbatar da an yi adalci ga wadanda abin ya shafa.
Miyetti Allah ta kare Fulani daga zargi
Sai dai shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar Nasarawa, Bala Dabo, ya musanta zargin cewa Fulani makiyaya ne suka kai harin a Kunza.
Bala Dabo ya amince cewa an kai hari, amma ya ce babu hujja da ke nuna cewa Fulani ne suka aikata shi.
Ya zargi wasu kabilu a yankin da toshe hanyoyi tare da kai hari kan Fulani, inda suke zarginsu da hannu a tashin hankalin.
A cewarsa, bincike ya nuna cewa an kai wa Fulani uku hari a ranar kasuwa, aka kashe daya daga cikinsu, amma iyalan wadanda abin ya shafa ba su bayyana sunayen maharan ba ko danganta lamarin da wata al’umma.

Source: Original
'Yan sanda sun tabbatar da harin
A halin da ake ciki kuma, rundunar ’yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da harin da aka kai a kauyen Kunza Ashigye, inda ta ce mutane uku sun mutu, yayin da mutane tara suka jikkata.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin, tare da tura jami’an tsaro na musamman zuwa yankin.
'Yan bindiga sun sace tsohon dan majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon dan majalisar wakilai a jihar Ogun.
Maharan dauke da makamai sun sace Hon. Maruf Musa, a yankin Ibiade da ke karamar hukumar Ogun Waterside ta jihar.
Majiyoyi sun ce an sace tsohon ɗan majalisar ne yayin da yake tsaka da ibadar sallar Magriba da misalin karfe 7:00 na yamma, a wani masallaci da ke cikin harabar gidansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



