'Yan Bindiga Sun Kutsa har Gida, Sun Kashe 'Dan'uwan Hadimar Gwamna a Jihar Kaduna
- 'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun kashe dan uwan daya daga cikin hadiman Gwamna Malam Uba Sani na jihar Kaduna
- Rahoto ya nuna cewa 'yan ta'addan sun hallaka 'dan uwan Mai ba gwamnan Kaduna shawara kan harkokin siyasa, Rachel Averik
- Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa tuni jami'anta suka fara bincike kan lamarin, wanda ya auku a karamar hukumar Sanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Miyagun 'yan bindiga sun kai wani mummunan hari tare da kashe 'dan'uwa ga daya daga cikin hadimin Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe Kefas Habila Averik mai shekara 33, ɗan’uwan Rachel Averik, wacce ke riƙe da mukamin Mai Ba Gwamnan Kaduna Shawara kan Harkokin Siyasa.

Source: Original
Maharan sun tafka wannan aika-aika ne a kauyen Hayin Gada da ke gundumar Arak 1, a Karamar Hukumar Sanga ta jihar Kaduna, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
An kashe dan'uwan hadimar gwamna
An ruwaito cewa yan ta'addan sun kai hari gidan marigayin, inda suka bude wuta tare da kiran Kefas da ya buɗe ƙofa, a lokacin da yake cikin ɗaki tare da matarsa, Joy da yaronsa.
Mazauna yankin sun bayyana cewa lokacin da Kefas ya ƙi buɗe ƙofar, ‘yan bindigan sun fasa taga, suka shiga ɗakin, sannan suka harbe shi a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take.
Wani mazaunin yankin ya ce harin ya faru ne da tsakar dare, wayewar garin ranar Laraba 31 ga Disamba, 2025.
“Lamarin ya faru ne da safiyar yau. Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun shigo garin yayin da mutane ke barci. Kai tsaye suka nufi gidan Kefas Habila Averik suka harbe shi.
“Yana cikin ɗaki tare da matarsa da yaro lokacin da suka zo. Sun umarce shi da ya buɗe ƙofa amma ya ƙi. Sai suka fasa taga, suka harbe shi, sannan suka tsere,” in ji shi.
Wane mataki hukumomi suka dauka?
‘Yar’uwar marigayin kuma Mai Ba Gwamna Uba Sani Shawara kan Harkokin Siyasa, Rachel Averik, ta tabbatar da faruwar lamarin, cewar Daily Post.
“An sanar da ni wannan mummunan al’amari mai tayar da hankali. An gaya mini cewa ya umurci matarsa da ta kai yaron su cikin banɗaki su ɓuya lokacin da ‘yan bindigar ke ƙoƙarin shiga ɗakin.
"Sun rika haska fitilu na tsawon lokaci, shi kuma Kefas yana ihu, amma babu wanda ya fito domin ‘yan bindigar suna harbi,” in ji Rachel.

Source: Twitter
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya shaida wa manema labarai cewa za su gudanar da bincike kan lamarin, kuma za su fitar da ƙarin bayani nan gaba.
Yan bindiga sun sace fasto a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa ‘yan bindiga sun sace faston Katolika mai suna Emmanuel Ezema, na cocin St. Peter’s da ke unguwar Rumi, cikin jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga har cikin gidan faston da ke harabar cocin, kana suka tasa shi zuwa cikin daji.
Sace Faston ya faru ne a lokacin da matsalolin tsaro suka ƙaru a faɗin ƙasar, musamman hare-haren da ake kai wa al’umma da malaman addini.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


