Yadda Hare Haren Sojoji ke Raunana ’Yan Bindiga, Sun Shiga Bala’i a Zamfara

Yadda Hare Haren Sojoji ke Raunana ’Yan Bindiga, Sun Shiga Bala’i a Zamfara

  • Rundunar Sojin Sama ta Najeriya na ci ga gaba da ƙaddamar da hare-haren sama masu ƙarfi kan yan bindiga a Zamfara
  • Majiyoyin tsaro sun ce lamarin ya tarwatsa manyan sansanonin ‘yan bindiga inda mayakan suka shiga bala'i
  • Hare-haren sun hallaka ‘yan bindiga da dama tare da lalata makaman yaƙi, hanyoyin samar da kayayyaki da maboyarsu a Tsafe da Maru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Hare-haren sama da Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya na ci gaba da zama bala'i ga yan ta'adda a Zamfara.

Rahotanni sun ce hare-haren sun yi matuƙar raunana ‘yan bindiga a Jihar da wasu sassan da ke makwabtaka da ita, inda hakan ya jefa ragowar ‘yan ta’addan cikin ruɗani da firgici.

An ce hare-haren sojoji a Zamfara yana tarwatsa yan ta'adda
Ministan tsaro, Christopher Musa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Yadda sojoji ke raunata yan bindiga a Zamfara

Kara karanta wannan

Sojoji sun damƙe ƴan ƙunar baƙin wake 2 kan tashin bam a masallacin Maiduguri

Majiyoyin tsaro sun shaidawa Tribune cewa hare-haren sama da ake kaiwa bisa sahihan bayanan sirri a ƙarƙashin ayyukan yaƙi da ‘yan bindiga sun tarwatsa muhimman sansanoninsu.

A cewarsu, hare-haren sun lalata tsarin jagorancinsu tare da hana su walwala da ‘yancin tafiye-tafiye a fadin yankin Arewa maso Yamma.

Majiyar ta bayyana cewa hare-haren da aka kai kwanan nan a ƙananan hukumomin Tsafe da Maru sun hallaka ‘yan bindiga da dama tare da lalata muhimman kayayyakin aikinsu, ciki har da ma’ajiyar makamai, hanyoyin samar da kayayyaki da wuraren buya.

Ya ce:

“Tasirin wadannan hare-haren sama da ake ci gaba da kaiwa ya yi matuƙar girma. Ƙungiyoyin ‘yan bindiga sun tarwatse kuma sun yi rauni sosai, har ba sa iya shirya hare-hare masu tasiri.”
Yan bindiga suna ganin ta kansu a Zamfara bayan hare-haren sojoji
Taswirar jihar Zamfara da ke shan fama da matsalar yan ta'adda. Hoto: Legit.
Source: Original

'Faragabar da yan ta'adda ke ciki a Zamfara'

Majiyar ta ƙara da cewa sahihan bayanan sirri sun nuna wasu daga cikin ƙungiyoyin ‘yan bindiga, bayan asarar rayuka da kayan aiki, suna roƙon a dakatar da hare-haren sama tare da neman tattaunawa.

A cewar majiyar, wannan alama ce ta matsanancin fargaba da rushewar kwarin gwiwarsu, tana mai cewa hare-haren sama ya karkatar da al’amura ƙwarai zuwa ga ɓangaren Sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Makaman da Amurka ta harbo Najeriya sun kara tona asirin Gwamnatin Bola Tinubu'

Har ila yau, majiyar ta jaddada cewa wannan farmaki na nuna ingancin ƙarfin jiragen saman sojojin wajen tallafa wa sojojin ƙasa, tare da nuna ƙudurin Gwamnatin Tarayya na hana ‘yan ta’adda samun wuraren fakewa.

Ta tabbatar da cewa jami’an tsaro za su ci gaba da matsa lamba har sai an murƙushe ‘yan bindiga da sauran laifuffukan tashin hankali, tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a al’ummomin da abin ya shafa, cewar Daily Post.

An karyata hallaka Bello Turji

An ji cewa a safiyar ranar Lahadi 28 ga watan Disambar 2025 aka yada rade-radin harin Amurka da aka kai a Sokoto ya yi ajalin Bello Turji.

Amurka dai ta kai harin ne a ranar Kirsimeti kan wasu yan ta'adda da ta kira da yan kungiyar ISIS a wasu yankuna.

Masu bincike sun ce labarin kisan Turji ya samo asali ne daga bayanan bogi da suka dade da aka sake yadawa domin wata manufa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.