Gyare Gyare da Alkawuran da Majalisar Wakilai Ta Gaza Cikawa a 2025

Gyare Gyare da Alkawuran da Majalisar Wakilai Ta Gaza Cikawa a 2025

  • A farkon 2025, majalisar kasa ta dauki alkawura masu yawa kan sauye-sauyen kundin tsarin mulki da tsaro, amma karshen shekara ya zo da tambayoyi
  • Daga kudurin ‘yan sandan jihohi zuwa tanadin kujeru na musamman ga mata, an yi alkawari amma ba a kai ga kada kuri’a ba game da su a majalisar
  • Masu sa ido a kan harkokin siyasa na ganin gibin dake tsakanin alkawari da cika shi ya kara nuna kalubalen da ke gaban majalisar dokokin Najeriya a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – A farkon shekarar 2025, jama’a da masu ruwa da tsaki sun saka buri kan majalisar kasa, bayan shugabannin majalisar sun yi alkawarin kawo manyan sauye-sauye a harkokin mulki, tsaro da sauransu.

'Yan majalisar sun bayyana shekarar 2025 a matsayin lokacin da za a gyara dokoki masu muhimmanci da suka dade suna jiran a warware su.

Kara karanta wannan

Majalisa ta mika wa Tinubu bukatar janye aiwatar da sabuwar dokar haraji a 2026

Majalisar dokokin Najeriya
Wasu 'yan majalisa dokoki suna tattaunawa. Hoto: Abbas Tajudeen
Source: Facebook

Yayin da 2025 ke zuwa karshe, rahoton The Cable ya sun nuna cewa da ba a cika da dama daga cikin alkawuranda majalisar ta yi ba.

Gyaran kundin tsarin mulki ya tsaya a Majalisa

Rahotanni sun bayyana cewa gyaran kundin tsarin mulkin 1999 ya kasance a sahun gaba na alkawuran majalisar a 2025.

Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulki, ya bayyana cewa za a kammala aikin gyaran kafin karshen Disamba, 2025.

An shirya sauraron ra’ayoyin jama’a a fadin kasar, inda aka karbi takardu da shawarwari kan tsaro, shigar mata cikin siyasa da inganta tafiyar da mulki.

Duk da haka da kuma maimaita alkawuran da shugabannin majalisar suka yi, wannan shiri bai kai ga matakin kada kuri’a ba.

Kara karanta wannan

Bayan farmakin Amurka a Sokoto, mayakan ISWAP sun kai kazamin hari Yobe

Masu sharhi na ganin wannan jinkiri ya rage kwarin gwiwar jama’a, musamman ganin yadda batutuwan suka shafi rayuwar yau da kullum ke kara taruwa ba tare da warwarewa ba.

Tanadin kujeru ga mata da batun sarakuna

Daya daga cikin kudurorin da suka fi daukar hankali a 2025 shi ne tanadin kujeru na musamman ga mata a majalisar dokoki ta kasa.

Wani rahoton Punch ya nuna cewa ‘yan majalisa da dama sun amince cewa Najeriya na da matsala wajen bai wa mata damar wakilci, kuma sun yi alkawarin daukar matakin gyaran kundin tsarin mulki domin magance hakan.

Haka kuma, an yi alkawarin ayyana rawar da sarakunan gargajiya za su taka a cikin kundin tsarin mulki domin ba su damar bayar da gudumawa.

Shugaban majalisar wakilai
Shugaban majalisa, Abbas Tajudeen na wani jawabi. Hoto: Abbas Tajudeen
Source: Facebook

Masu goyon bayan kudurin, ciki har da Benjamin Kalu, sun ba da hujjar cewa sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa a tsaro da shugabanci.

Sai dai, kamar sauran kudurorin da aka karanta, wannan shiri ya kare ne majalisa ba tare da kada kuri’a ba balle a samu damar zartar da shi.

Batun kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Karuwar matsalolin tsaro sun kara karfin kira daga gwamnoni da wasu 'yan majalisa kan neman kafa 'yan sandan jihohi a kasar nan.

Duk da amincewa da tsananin matsalar tsaro, majalisar ta nuna shakku wajen daukar matakin karshe. Jinkiri ya mamaye tattaunawa, lamarin da ya bar kudurin a rataye duk da bukatarsa da aka nuna.

Majalisa ta nemi janye dokokin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jingine aiwatar da dokokin haraji.

Hakan na zuwa ne bayan korafi da jama'a duka yi bayan samun labarin cewa an sauya wasu bangarori na dokokin da majalisa ta amince da su.

Sai dai duk da kiran da aka yi, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa babu makawa wajen aiwatar da dokokin a ranar 1 da Janairun 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng