Bam a Masallaci: Wanda Ake Zargi Ya Fadi Makudan Kudi da Aka Ba Shi a Borno
- Dakarun Operation Hadin Kai sun cafke wani da ake zargin ɗan kunar bakin wake na Boko Haram ne a Najeriya
- Wanda ake zargin ya bayyana yadda aka shirya harin masallacin kasuwar Gamboru da ya kashe mutane biyar tare da jikkata 32
- Ya ce bayan fashewar bam din, ya koma wurin yana taimakawa, yana ɗaukar gawarwaki zuwa cikin motoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Wani da ake zargin ɗan kunar bakin wake na Boko Haram, mai suna Ibrahim Mohammed ya shiga hannun sojoji.
Dakarun Operation Hadin Kai ne suka kama tare da haɗin gwiwar mafarauta a Jihar Yobe inda ya yi tone-tone.

Source: Original
Matashi ya tona asirin kai harin bam a Borno
Rahoton Zagazola ya ce matashin ya fallasa yadda ake ɗaukar mutane, a biya su da tura su kai hare-haren kunar bakin wake a Arewa maso Gabas.
Ibrahim ya amsa cewa yana karɓar kuɗi daga ₦70,000 zuwa ₦100,000 a duk lokacin da aka ba shi aikin kai harin kunar bakin wake a kan masallatai da kasuwanni.
Da yake magana yayin bincike, Ibrahim ya ce shirin harin ya gudana ne bisa umarnin shugabannin Boko Haram da ke aiki tsakanin Jihar Adamawa da tsaunukan Mandara.
Ya bayyana cewa sukan yi anfani da lokutan da masallatai ke zama babu mutane domin dasa abubuwan fashewa.
Ya ce:
“Sunana Ibrahim daga Michika a Jihar Adamawa. Mun zo Maiduguri ne domin dasa bam a Masallacin Izala. Shugabanninmu Adamu da Abubakar ne suka aiko mu, suka ba mu bama-bamai guda biyu domin dasawa a masallacin.
“Mun shiga bayan sallar Azahar da La’asar lokacin da masallacin babu kowa. Mun shiga masallacin kamar muna sallah. Abokina yana haƙa rami a tsakiyar masallacin ni kuma ina haƙa a gefe.”

Source: Twitter
Yadda aka tarwatsa masallaci a Borno
Ibrahim ya ce an haɗa bama-baman tare da saita su domin fashewa kafin sallar Magariba.
Abin da ya ƙara tayar da hankali shi ne furucinsa na cewa bayan fashewar bam, ya koma wurin yana taimakwa yan gari kwashe gawarwaki.
Ya ƙara da cewa:
“Yayin da jama’a suka taru domin sallar Magariba, bayan raka’a ta farko, bama-baman suka tashi. Mun sa lokacin minti biyar. Bayan haka na gudu zuwa kasuwa.
“Da na koma masallacin, ana kwashe gawarwaki. Na taimaka wajen ɗaukar gawarwaki zuwa motoci.”
Ibrahim ya bayyana cewa aikin kunar bakin wake ya zama kasuwanci a cikin ƙungiyoyin ta’addanci, yana mai cewa:
“Ana biya na kuɗi tsakanin ₦70,000 zuwa ₦100,000 a kowane aiki.”
Sai dai ya ce yanzu yana nadama, yana mai bayyana rashin jin dadi kan kashe mutanen da ba su aikata laifi ba.
Bayan harin Gamboru, Ibrahim ya ce ya wuce Jihar Yobe domin gudanar da bincike da leƙen asiri kan wuraren sojoji da ƙungiyoyin mafarauta, domin shirya ƙarin hare-hare.
Ya ce:
“Bayan wannan aiki, na je Yobe domin wani aiki na daban, domin duba wuraren sojoji da na mafarauta don kai hare-hare kan sababbin sojoji.”
Bam: Matakan da Sojojin Borno suka dauka
Mun ba ku labarin cewa Rundunar Sojoji ta tabbatar da kai harin bam masallaci da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri yayin sallar Magariba.
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin wani dan kunar bakin wake daga kungiyar Boko Haram ne ya tayar da bam din.
Rundunar ta ce ta dauki matakan gaggawa tare da kara tsaurara tsaro domin hana sake aukuwar irin wannan hari.
Asali: Legit.ng


