Babban Sarki Ya Bar Duniya Kwana 1 kafin Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa
- Al'umma sun shiga wani irin yanayi bayan sanar da rasuwar babban basarake ana shirin bikin ranar haihuwarsa
- Marigayin Mai Martaba Igwe PD Uzochukwu ya bar duniya ne a Enugu kwana guda kafin cikar sa shekara 90 a duniya
- Mutanen Mgbidi sun bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga al’ummarsu da ci gabanta duba da gudunmawarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Enugu - An shiga tsananin alhini a Jihar Enugu bayan rasuwar Sarkin Ezineze Mgbidi, Mai Martaba Igwe PD Uzochukwu (Ezudo I na Mgbidi).
Basaraken ya rasu kwana guda kafin bikin cikar sa shekara 90 a duniya da kuma zagayowar shekaru 38 da na nadin sarauta.

Source: Original
An yi rashin babban Sarki a Najeriya
Rahoton Vanguard ya ce rasuwar ta faru ne a yankin Awgu da ke ƙaramar hukumar Awgu ta Jihar Enugu, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da kaduwa.
Majiyoyi sun nuna cewa an riga an fara shirye-shiryen babban bikin da aka tsara yi a ranar Laraba, 31 ga Disamba, 2025, inda aka kafa alluna masu ɗauke da sanarwar bikin a sassan yankin.
Jama’a da dama ma sun riga sun dawo gida domin halartar bikin kafin labarin rashin lafiyar Sarkin ya bazu.
Wani ɗan Sarkin, Yarima Emeka Uzochukwu, ya tabbatar da rasuwar, inda ya bayyana cewa fadar ba ta taɓa tsammanin mutuwar Sarkin ba.
A cewarsa, marigayin ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Enugu, lamarin da ya girgiza iyalansa da al’ummarsa baki ɗaya.
Yarima Emeka ya ce:
“Kasancewa tare da shi a asibiti kafin rasuwarsa, abu ne mai matuƙar wahala mu yarda cewa Igwe ya riga ya tafi ya bar mu.”

Source: Twitter
Halin da yan yankin marigayin ke ciki
A matsayin girmamawa, al’ummar yankin sun nuna jimami tare da yin shiru na minti ɗaya yayin wani taron jama’a da aka gudanar a makarantar Mgbidi.
Shugaban Ƙungiyar Mgbidi, Barrista Theophilus Nzeh, ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga ƙananan hukumomi biyu masu cin gashin kansu a Mgbidi.
Ya yabawa marigayi Sarkin bisa jajircewarsa, hangen nesa da gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa al’ummarsa.
An bayyana cewa Igwe Uzochukwu, wanda ya hau karagar mulki shekaru 38 da suka wuce, ya gaji Cif G. I. Oko, sannan ya jagoranci rabuwar Mgbidi zuwa ƙananan hukumomi biyu masu cin gashin kansu, Ezineze Mgbidi da Ezineri.
Za a ci gaba da tunawa da marigayin a matsayin jagora nagari, mai hangen nesa da jajircewa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar jama’arsa da ci gaban yankinsa.
Jigon APC kuma Sarki ya rasu
Kun ji cewa an tabbatar da rasuwar Sarkin Igbajo na 30 kuma tsohon shugaban APC reshen jihar Osun, Oba Adegboyega Famodun.
Iyalan gidan sarauta na Gbeleru sun bayyana cewa marigayin ya rasu ranar Juma'a bayan gajeruwar jinya, yana da shekaru 67.
Oba Famodun ya zama Sarki a 2022 lokacin mulkin APC a jihar Osun amma bayan zuwan Gwamna Adeleke, ya fara fuskantar matsala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
