'An Fara Ruwan Kudi': Gwamna Ya Biya Ma'aikata Albashin Watan 13 bayan Kirsimeti
- Gwamna Monday Okpebholo ya biya ma'aikatan jihar Edo albashin wata 13 domin rage musu radadin hidimomin karshen shekara
- Ma'aikata sun nuna farin ciki da samun tallafin wadanda suka ce za su taimaka musu wajen biyan kudin makarantar yara da hayar gida
- Gwamnati ta bayyana dalilin da ya sanya Gwamna Okpebholo ya ƙaddamar da irin wannan tsarin na biyan albashin wata 13 a 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya sanya farin ciki a zukatan ma'aikatan gwamnatin jihar ta hanyar biyan su albashin watan 13.
Ma'aikata daga ma'aikatu daban-daban, da suka haɗa da na yaɗa labarai, filaye da gidaje, muhalli, da kuma ilimi, sun tabbatar da samun saƙon banki na wannan kuɗi, inda suka bayyana matakin a matsayin wanda ya zo a daidai gaba kuma zai ƙara musu karsashin aiki.

Source: Twitter
Ma'aikata sun samu albashin wata 13
Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Mista Patrick Ebojele, ne ya tabbatar da hakan ga jaridar The Punch, inda ya ce wannan karamci shaida ce ta manufofin gwamnan na tallafawa ma'aikata.
Ya bayyana cewa Okpebholo ya ƙaddamar da wannan tsarin na biyan albashin wata 13 makonni kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin gwamna a watan Nuwamba 2024.
A cewar hadimin gwamnan, Okpebholo ya kuma ci gaba da hakan a wannan shekarar domin rage wa ma'aikata raɗaɗin hidimomin ƙarshen shekara da shiga sabuwar shekara.
Gwamna ya yi wa ma'aikata albashin ba-zata
Darakta a ma'aikatar yaɗa labarai, Mrs. Rose Imonikhe, ta bayyana cewa wannan kuɗi ya zo musu a daidai lokacin da ba su yi tsammani ba, in ji rahoton The Nation.
Ta ce samun kuɗin zai taimaka wa ma'aikata sosai, musamman waɗanda suka riga suka kashe albashinsu na watan Disamba wajen hidimar Kirsimeti.
A cewar Mrs. Rose, yanzu ma'aikatan Edo sun samu kuɗin biyan kuɗin makarantar yara da kuma sabunta kuɗin hayar gida a farkon shekara ba tare da fuskantar matsin lamba ba.

Source: Twitter
Albashi: Ma'aikata sun jinjina wa gwamna
Sauran ma'aikata irinsu Mrs. Bridget Igbinovia da Onyinyechi Florence sun kwatanta biyan albashin a matsayin nuna damuwa ta zahiri ga jin daɗin ma'aikata daga gwamnan.
Haka kuma, daraktar gudanarwa a ma'aikatar muhalli, Mrs. Egbe Jocy, ta jaddada cewa wannan mataki zai ƙarfafa gwiwar ma'aikata tare da haɓaka ayyuka a dukkan sassan gwamnatin jihar.
Gaba ɗaya ma'aikatan sun nuna gamsuwarsu da tsarin mulki na Gwamna Okpebholo wanda suka ce yana mayar da hankali ga walwala da ci gaban talakawan Edo.
Gwamna ya sake karawa ma'aikata albashi
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Monday Okpebholo ya amince da sabon mafi karancin albashi na ₦75,000 ga ma’aikatan jihar Edo.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta mayar da daruruwan ma’aikatan wucin-gadi zuwa cikakkun ma’aikata, tare da ɗaukar sababbin malamai da ma’aikatan lafiya.
Monday Okpebholo ya kuma yaba da jajircewar ma’aikata a fannoni daban-daban, ya kuma ce gwamnati na kokarin magance ƙalubalen da suke fuskanta.
Asali: Legit.ng

