Jihohin Najeriya 10 da za Su Ci Bashin Naira Tiriliyan 4.287 a 2026
- Jihohi 10 a Najeriya sun gabatar da tsare-tsaren kasafin kuɗin 2026 da ke nuna dogaro da bashin kuɗi da wasu hanyoyin samun kuɗi na wucin gadi
- Masana tattalin arziki sun yi gargadi cewa yawaitar karɓar bashi na iya haifar da matsaloli, musamman idan ba a gyara matsalolin sarrafa kuɗin gwamnati ba
- Rahotanni sun nuna bambance-bambance a tsakanin jihohi, inda wasu gwamnoni ke ƙara bashi yayin da wasu ke ƙoƙarin rage nauyin bashin da ke kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jihohi 10 a Najeriya sun bayyana shirin samo kimanin Naira tiriliyan 4.287 daga bashin kuɗi, tallafi da sauransu domin ɗaukar nauyin ayyukan raya ƙasa a kasafin kuɗin shekarar 2026.
Wani rahoton nazari kan kasafin kuɗin ya nuna cewa jihohin sun gabatar da kasafin kuɗi da ya kai jimillar Naira tiriliyan 14.174, lamarin da ke nuna ƙaruwa a dogaro da hanyoyin samun kuɗi da ba na dindindin ba.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Lagos, Abia, Ogun, Enugu, Osun, Delta, Sokoto, Edo, Bayelsa da Gombe, inda kowace jiha ke neman wata dabara ta musamman domin cike gibin kuɗin yin ayyuka.
Me ya sa jihohi ke ciwo bashi?
Binciken ya nuna cewa jihohin na ƙara juyawa zuwa bashin kuɗi ne saboda karancin kudin shigar da suke samu daga rabon tarayya, harajin VAT da kuma kudin shiga na cikin gida.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa matsalar ba ƙarancin kuɗi ba ce, illa rashin sarrafa kuɗin gwamnati yadda ya dace. Sun ce kasafin kuɗi, wanda ya kamata ya zama ginshiƙin kashe kuɗi, sau da yawa ba a bin sa yadda ya dace.
Tsohon shugaban jami’ar Crescent, Farfesa Sheriffdeen Tella, ya yi kira ga jihohi da su koyi rayuwa gwargwadon ƙarfin su tare da ƙara inganta hanyoyin samun kudin shiga na cikin gida.

Kara karanta wannan
Kamfanin JED ya nemi masallatai da coci su rika biyan kudin lantarki a jihar Gombe
Kasafin Lagos da jihar Abia
Rahoton Vanguard ya nuna cewa a jihar Lagos, gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gabatar da kasafin kuɗi na N4.237tn na shekarar 2026.
Daga cikin wannan adadi, ana sa ran N3.12tn za su fito ne daga kudin shiga na cikin gida da rabon tarayya, yayin da za a samo N1.117tn ta hanyar bashi domin ayyukan raya ƙasa.
Duk da kasancewar Lagos na da kudin shiga da suka kai na wasu ƙananan ƙasashen Afirka, rahoton ya nuna cewa bashi har yanzu na taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manyan ayyuka a jihar.

Source: Facebook
A Abia kuwa, kasafin kuɗin N1.016tn ya bar gibin N409bn da ake shirin cike wa ta hanyar bashi da sauran hanyoyin samun kuɗi na wucin gadi.
Abubuwan da za su faru a 2026
A wani labarin, mun hada muku rahoto na musamman game da wasu muhimman abubuwan da za su faru a Najeriya a shekarar 2026.
A farkon 2026 ne gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu za ta fara aiwatar da sababbin dokokin haraji da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu.
Haka zalika, attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote zai fara raba man fetur kyauta ga abokan huldarsa a watan Janairun shekarar 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

