'Ba Mu So': 'Yan Majalisa Sun Fusata da Gwamnati Ta Tura Masu Kyautar N100,000

'Ba Mu So': 'Yan Majalisa Sun Fusata da Gwamnati Ta Tura Masu Kyautar N100,000

  • 'Yan majalisar Rivers sun ki karbar N100,000 na kyautar Kirsimeti da aka ce Gwamna Simalayi Fubara ya rabawa ma'aikata a jihar
  • Majalisar ta zargi gwamnan da yin amfani da kudaden jihar ba tare da amincewar su ba, wanda hakan ya saba kundin tsarin mulki
  • An umurci mambobin majalisar da su gaggauta mayar da kudaden yayin da rikicin siyasa tsakanin gwamna da majalisa ke kamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - 'Yan majalisar dokokin jihar Rivers sun ki karbar N100,000 da aka tura wa kowannensu a matsayin kyautar Kirsimeti, bisa umarnin Gwamna Siminalayi Fubara.

A cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa ba ta nemi gwamnati ta tura mata wannan kudi ba kuma bai samu sahalewar masu yin doka a jihar ba.

Kara karanta wannan

An samu sababbin bayanai game da 'tashin bam' a asibitin Kebbi

Majalisar Rivers ta ce za ta mayar da N100,000 da gwamna ya ba mambobinta kyauta.
Ginin majalisar dokokin jihar Rivers (hagu) da Gwamna Siminalayi Fubara (dama). Hoto: @rvhaofficial, @SimFubaraKSC
Source: Twitter

'Yan majalisa sun ki karbar kyautar N100,000

'Yan majalisar sun kuma jaddada cewa dole ne gwamna ya kiyaye tsaro na doka da neman amincewar majalisa kafin ya kashe duk wani kudi na gwamnati, in ji rahoton Punch.

Yayin da ma'aikatan gwamnatin jihar ke cikin murna sakamakon samun wannan kyautar N100,000 daga Fubara, shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Enemi George, ya bayyana cewa tura wa 'yan majalisa waɗannan kuɗaɗen ya saɓa wa ƙa'ida.

George ya zargi gwamnan da ci gaba da amfani da asusun harajin jihar ba tare da amincewar majalisa ba tun bayan rantsar da shi a 2023, sannan ya bayyana cewa mambobin majalisar sun fara daukar matakan mayar da kuɗaɗen ga asusun gwamnati.

Rikicin shari'a da na kasafin kuɗi a Rivers

Bayanai sun nuna cewa har yanzu Gwamna Fubara bai gabatar da kasafin kuɗin 2026 ga majalisar ba don dubawa da amincewa, sannan kuma bai miƙa sunayen kwamishinonin da majalisar ta nema ba.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kai kazamin hari a Kebbi

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnan yake gudanar da harkokin gwamnati da kwamishinoni takwas kacal waɗanda hukuncin Kotun Ƙoli bai shafa ba.

Hukuncin kotun ne da ya amince da Martin Amaewhule a matsayin halastaccen shugaban majalisar dokokin jihar Rivers.

Majalisar dokokin jihar Rivers ta umarci mambobinta su mayar da kyautar N100,000 da gwamna ya ba su.
Ginin majalisar dokokin jihar Rivers, inda ake adawa da kyautar N100,000 da gwamna ya ba 'yan majalisa. Hoto: @rvhaofficial
Source: Twitter

Majalisar Rivers ta gargadi wasu jami'an gwamnati

Majalisar ta kuma yi gargaɗi ga wasu ma'aikatan gwamnati da ke haɗa baki da Gwamna Fubara wajen karya tsarin mulki da dokokin jihar Rivers, in ji rahoton Leadership.

Enemi George ya tabbatar wa al'ummar jihar cewa majalisar za ta ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da bin doka da oda da kuma raba madafun iko.

Majalisar ta ɗage zamanta zuwa ranar 26 ga Janairu, 2026, yayin da takaddama tsakanin ɓangaren zartarwa da na doka ke ci gaba da ƙaruwa.

'Yan majalisa 16 sun watsar da PDP a Rivers

A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Rivers sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

Mambobin majalsiar 16 sun sanar da yanke shawarar shiga jam'iyyar APC mai mulki, a wani sauyin siyasa da ya girgiza majalisar tun bayan cire dokar ta baci.

Kakakin majalisar, Martin Amaewhule, ya ce zai yi duk abin da ya dace domin samun katin APC cikin gaggawa, yana mai cewa yanzu haka ya zama cikakken mamba na jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com