Za a Fara Cire Haraji a Asusun Masu Tura Kuɗi daga Watan Janairun 2025

Za a Fara Cire Haraji a Asusun Masu Tura Kuɗi daga Watan Janairun 2025

  • Sabon haraji da gwamnatin tarayya ta kawo zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disambar 2025 musamman wadanda suka shafi bankuna
  • Daga 1 ga Janairu, 2026, bankuna za su fara cire ₦50 harajin hatimi kan duk wata tura kuɗi tdaga ₦10,000 zuwa sama
  • Sabon tsarin ya tanadi cewa wanda ya tura kudin ne zai biya harajin, ba mai karɓa ba kamar yadda aka saba a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Bankuna za su fara cire kudi a asusun wadanda suka tura kudi daga 1 ga watan Janairun 2026.

An ce ranar 1 ga Janairu, bankuna a Najeriya za su fara cajin ₦50 harajin hatimi ga masu tura da kuɗi idan adadin kuɗin ya kai ₦10,000 ko fiye.

Bankuna za su fara cire haraji daga watan Janairun 2025
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Za a fara cire harajin hatimi a 2026

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ana zargin uwargida ta hallaka mijinta saboda ya yi mata kishiya

Rahoton TheCable ya tabbatar da cewa hakan ya biyo bayan fara aiwatar da sabuwar dokar haraji ta gwamnatin tarayya, cewar Vanguard.

Harajin hatimi, wanda ake kira Electronic Money Transfer Levy (EMTL), cajin kuɗi ne guda ɗaya na ₦50 da ake cirewa a duk karɓa ko aikawa da kuɗi.

Za a cire kudin a kowane asusu da ke cikin banki ko wata cibiyar kuɗi, muddin adadin ya kai ₦10,000 zuwa sama.

Yadda tsarin cire kudi a bankuna zai kasance

A cikin wani saƙon imel da United Bank for Africa (UBA) ya aikawa abokan hulɗarta, bankin ya bayyana cewa harajin EMTL yanzu za a kira shi 'stamp duty' a dukkanin cibiyoyin kuɗi.

A cewar saƙon:

“Ku lura cewa harajin hatimi yana aiki ne ga duk wata mu’amala ta kuɗi da ta kai ₦10,000 ko fiye (ko makamancin haka a wasu kuɗaɗe).”

Har ila yau, sakon ya fayyace cewa cire kudin ba zai shafi albashin da ke shigowa asusun bankin abokan hulda ba.

"Ban da biyan albashi da tura kuɗi a cikin banki ɗaya ga kai da kanka (intra-bank self-transfer)"

Kara karanta wannan

AFCON 2025: Wasu fitattun 'yan wasan Najeriya 4 na fuskantar dakatarwa

Bankin UBA ya tura sakkonni kan fara cire haraji a 2026
Ginin bankin UBA da ke hada-hadar kudi. Hoto: UBA.
Source: Getty Images

Bankin UBA ya yi karin haske kan harajin

UBA ya ƙara da cewa sabon tsarin ya tanadi cewa mai aikawa da kuɗi ne zai biya harajin hatimi, sabanin tsarin da aka saba a baya inda ake cire kuɗin daga mai karɓa.

Bankin ya jaddada cewa yana ci gaba da jajircewa wajen bayyanawa da sanar da kwastomomi duk wani sauyi da zai shafi mu’amalolinsu na banki.

A baya, ranar 7 ga Satumba, 2024, kamfanonin fasahar kuɗi (fintechs) a Najeriya sun sanar da shirin fara cajin ₦50 harajin hatimi kan duk wata mu’amala ta ₦10,000 zuwa sama, inda suka ce hakan ya dace da dokokin Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS).

Majalisa ta roki Tinubu kan dokar haraji

Kun ji cewa Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da batun fara aiwatar da dokar haraji a watan Janairun 2026.

An nemi a dakatar da aiwatar dokokin ne bayan surutu ya yi yawa game da zargin cewa akwai bambanci tsakanin wacce Majalisa da gyara da wacce aka sa wa hannu.

Tuni majalisa ta kafa kwamiti da zai bibiyi lamarin, domin gano yadda aka samu matsala a dokokin harajin da ake cece-kuce a kansu a 'yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.