Haraji: A kowane mako, mu na tatsar N3bn a dalilin kudin hatimi – Nami

Haraji: A kowane mako, mu na tatsar N3bn a dalilin kudin hatimi – Nami

- Majalisa ta gayyaci NIPOST da FIRS a dalilin sabanin da su ka samu

- Kowace hukuma ta na ikirarin ta na da hakki da kudin harajin hatimi

- Hukumar FIRS ta shaidawa Majalisa irin kudin da ake samu da harajin

Hukumar FIRS mai tara haraji a Najeriya ta ce kimanin Naira biliyan uku ta ke samu duk mako daga harajin hatimi da ta ke karba a kasar.

Shugaban hukumar FIRS,Muhammad Nami ya bayyana wannan a wata ganawa da ya yi da ‘yan majalisar tarayya a ranar Talata, 11 ga watan Agusta.

Malam Muhammad Nami ya bayyana ne a gaban kwamitin kudi na majalisar wakilai a game da sabanin da hukumarsa ta ke samu daga NIPOST.

Nami ya ce a sanadiyyar wata sabuwar manhaja da su ka kawo domin inganta tatsar harajin hatimi, yanzu su na samun Naira biliyan uku a kowane mako.

Wannan manhaja kamar yadda Malam Nami ya shaidawa ‘yan majalisa, ta kawo fasahar da ta saukaka yadda su ke aikin karbar harajin hatimi a kasar.

KU KARANTA: Ya kamata a binciki tsohon Mataimakin Gwamnan CBN - Bukarti

Haraji: A kowane mako, mu na tatsar N3bn a dalilin kudin hatimi – Nami
Kwamitin Majalisa a bakin aiki
Asali: Twitter

Shugaban na FIRS ya ke cewa a lokacin da ya shiga ofis, Naira biliyan 30 ne kacal a asusun NIPOST na tara kudin hatimi a cikin a babban bankin CBN.

A cewar Nami, daga wancan lokaci zuwa watan Afrilun 2020, abin da ke asusun NIPOST ya kai Naira biliyan 58 saboda wannan manhaja da aka kawo.

Jaridar Vanguard ta rahoto Malam Muhammad Nami ya na cewa tun shekaru 94 da su ka wuce, hukumomin haraji ne su ke da alhakin karbar kudin hatimi.

FIRS ta nuna rashin jin dadi game da yadda sabaninta da NIPOST ya fito karara.

Idan ba za ku manta ba, kwanakin baya hukumomin sun fito su na musayar kalamai.

Shugaban NIPOST, Dr. Ismail Adewusi, ya yi karin haske, ya kuma yarda da Nami a kan wannan batu. A karshe majalisa ta ce za ta duba yadda za a cin ma masalaha.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng