Ana Rade Radin zuwan Abba Kabir APC, Ganduje Ya Tura Masa Saƙo kan Sauya Sheka
- Tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana yayin da ake ta maganganu a kan siyasar Kano
- Dr. Abdullahi Ganduje musamman ya gayyaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya shigo jam’iyyar APC mai adawa a Kano
- Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya ce APC a shirye take ta karɓi Gwamna Abba domin haɗin kai da ci gaban jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano – Jam’iyyar APC a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta magantu kan siyasar jihar.
Abdullahi Ganduje ya gayyaci magajinsa, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya bukace shi da ya dawo jam’iyyar mai mulki.

Source: Twitter
Shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Talata 30 ga watan Disambar 2025, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Kalu: Mataimakin shugaban majalisa ya fara zawarcin gwamna 1 na jam'iyyar LP zuwa APC
Mahangar Kwankwaso kan 'shigan' Abba APC
A cewar rahotanni, shirin da ake cewa Gwamna Abba Kabir na sauya sheƙa zuwa APC ya haifar da rarrabuwar kai a jam’iyyar NNPP, wadda a ƙarƙashinta aka zaɓe shi gwamna.
Jagoran NNPP na ƙasa kuma mai gidan Gwamna Abba, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bai goyi bayan shigarsa APC ba, inda ake ganin yana adawa da wannan mataki.
Dalilin jam'iyyar APC na gayyatar Abba Kabir
Da yake magana a madadin Ganduje, Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa shirin shigowar Gwamna Yusuf APC yana da nasaba da haɗin kai, sulhu da kuma muradin al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.
Abbas ya jaddada cewa gayyatar da APC ta yi wa Gwamna Yusuf na da manufar gina Kano mai haɗin kai, ta hanyar haɗa ƙarfi da tunani domin ci gaban jihar.
Ya ce:
“APC a shirye take ta karɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf hannu bibbiyu domin mu haɗa ƙarfinmu tare don ci gaban Jihar Kano.”

Source: Facebook
Yadda APC ta shirya karbar Abba Kabir
Dan Sarki ya ƙara da cewa, idan Gwamna Yusuf ya shigo APC a hukumance, shi da sauran manyan ’yan NNPP da za su biyo bayansa za a karɓe su cikin jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, cikin yanayi na mutunta juna.
Ya bayyana cewa APC na da burin ganin an samu hadin kan siyasa da zaman lafiya a Kano, tare da tabbatar da cigaba mai dorewa ga al’ummar jihar, cewar Daily Post.
Lamarin dai na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Kano, yayin da ’yan siyasa da magoya baya ke bibiyar ko Gwamna Abba Kabir Yusuf zai amince da wannan gayyata daga APC.
NNPP ta dakatar da shugaban dattawanta a Kano
Kun ji cewa jam’iyyar NNPP ta sanar da dakatar da Shugaban dattawan jam’iyyar a ƙaramar hukumar Ungogo, Alhaji Sammani Muhammad Zango.
Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso, jigo a tafiyar Kwankwasiyya, ne ya bayyana matakin dakatarwar saboda zargin rashin biyayya.
Wannan lamari na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rade-radin Abba Kabir Yusuf zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
