Rundunar Ƴan Sanda Ta Cafke fiye da Mutane 3,000 a Kano, Kwamishina Ya Yi Bayani

Rundunar Ƴan Sanda Ta Cafke fiye da Mutane 3,000 a Kano, Kwamishina Ya Yi Bayani

  • Rundunar yan sandan Kano ta kama mutane fiye da 3,000 da ake zargi da aikata fashi da makami, gakuwa da mutane da ayyukan daba
  • Jami'an hukumar sun kwace bindigogi sama da 90 da motoci da babura masu yawa tare da ceto wadanda aka yi garkuwa da su a 2025
  • Kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana shirin da rundunar ta yi don kare rayuka da dukiyoyi a 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ƙarƙashin CP Ibrahim Adamu Bakori, ta fitar da rahoton nasarorin da ta samu a 2025, ciki har da kama mutane 3,081 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka.

Wannan rahoto, ya nuna yadda rundunar ta baza komarta a dukkan sassan jihar domin kakkabe ɓata-garin da ke neman jefa jihar cikin rashin zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Fusatattun mutane sun farmaki ofishin hukumar NSCDC a Kano, an rasa rayuka

'Yan sandan Kano sun cafke fiye da mutane 3,000 a 2025 bisa laifuffuka daban daban.
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Bakori (dama) da jami'an rundunar (hagu). Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Twitter

'Yan sandan Kano sun fitar da rahoton 2025

CP Bakori ya bayyana cewa tun lokacin da ya kama aiki a ranar 17 ga watan Maris, 2025, ya gudanar da bincike na musamman domin gano tushen matsalolin tsaro a jihar, in ji rahoton Daily Trust.

Binciken ya nuna cewa fadan daba, kwace wayoyin hannu, da shaye-shayen miagun ƙwayoyi ne suka fi addabar cikin birni, yayin da yankunan iyakokin jihar 17 ke fuskantar barazanar shigowar ‘yan bindiga da rikicin manoma da makiyaya.

Sakamakon haka, rundunar ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna "Operation Kukan Kura," wanda ya ba jami'an tsaro damar yin katsalandan ga ayyukan masu laifi kafin su kai ga aikata su.

Kano: 'Yan sanda sun cafke mutane 3,081

A cikin kididdigar da rundunar ta bayar, an kama ‘yan daba guda 2,350, 'yan fashi da makami 146, da dillalan miagun ƙwayoyi 112. Haka kuma, an kama masu garkuwa da mutane 50 da ɓarayin motoci da babura sama da 250.

Kara karanta wannan

Malami: Kotu ta iza ƙeyar surukin Buhari da ɗansa zuwa gidan yarin Kuje

Wata babbar nasara da rundunar ta yi alfahari da ita ita ce ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun sami rauni ba.

Rundunar ta kuma yi nasarar ƙwace makamai masu yawa da suka haɗa da bindigogin AK-47 guda 9, ƙananan bindigogi 84, da harsashai 198, tare da kayan aikin ɓarayi kamar na'urorin POS da katinan ATM da ake amfani da su wajen damfara.

Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Bakori ya ce 'yan sanda za su kara kaimi a 2026
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kwamishinan 'yan sanda ya hango 2026

Kwamishina Bakori ya jaddada cewa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya ya taimaka ƙwarai wajen murƙushe ayyukan ta'addanci a yankunan iyaka.

Ya tabbatar wa mazauna jihar Kano cewa a shekarar 2026, rundunar za ta ƙara yin sintiri tare da amfani da na'urorin zamani wajen gano masu aikata laifuffuka ta yanar gizo, in ji rahoton Leadership.

Ya kammala da nuna godiya ga gwamnatin jihar Kano bisa goyon bayan da take ba rundunar, inda ya buƙaci jama'a su ci gaba da bayar da bayanai na sirri akan duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.

Fusatattu sun kona ofishin NSCDC a Kano

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kai kazamin hari a Kebbi

A wani labari, mun ruwaito cewa, fusatattun mutane sun cinnawa ofishin hukumar NSCDC wuta a Kano tare da kashe mutane uku da ake zargi da satar babura.

Kakakin rundunar NSCDC na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya cewa rikicin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Lahadi, 28 ga watan Disamba, 2025.

Yayin da jami’an NSCDC da ke bakin aiki suka sami nasarar tserewa daga ofishin da ke cin wuta, uku daga cikinsu sun sami raunuka kuma suna karɓar magani a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com