Fusatattun Mutane Sun Farmaki Ofishin Hukumar NSCDC a Kano, An Rasa Rayuka

Fusatattun Mutane Sun Farmaki Ofishin Hukumar NSCDC a Kano, An Rasa Rayuka

  • Wasu fusatattun mutane sun cinnawa ofishin hukumar NSCDC wuta a Kano tare da kashe mutane uku da ake zargi da satar babura
  • Jami'an tsaro uku sun jikkata yayin fafatawa da dandazon jama'ar da suka mamaye ofishin domin aiwatar da hukunci kan 'barayin'
  • Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan faruwar irin sa a jihar Katsina inda aka kashe mutane uku a wani ofishin hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar tsaro ta fararen hula (NSCDC) reshen jihar Kano, ta tabbatar da wani mummunan hari da wasu fusatattun mutane suka kai a ofishinta na Danmaje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.

Wannan hargitsi ya yi sanadiyyar kisan gilla ga mutane uku da ake zargi da aikata laifi, sannan kuma mutanen sun cinna wa ginin ofishin wuta har ya ƙone kurmus.

Kara karanta wannan

AFCON 2025: Wasu fitattun 'yan wasan Najeriya 4 na fuskantar dakatarwa

Fusatattun matasa sun kone ofishin NSCDC tare da kashe mutane 3
Jami'an hukumar NSCDC suna a bakin aiki. Hoto: @official_NSCDC
Source: Twitter

Kano: Rigima ta barke a ofishin NSCDC

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan faruwar irin sa a jihar Katsina inda aka kashe mutane uku a wani ofishin rundunar, a cewar rahoton Premium Times.

Kakakin rundunar NSCDC na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya cewa rikicin ya fara ne ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Lahadi, lokacin da mazauna yankin Yansango suka kawo wasu mutane uku da ake zargi da satar babura.

Jami’an sun karɓi waɗanda ake zargin domin gudanar da bincike, sai dai kafin a kai ga fara komai, dandazon jama’a daga ƙauyuka makwabta suka mamaye ofishin.

Mutanen sun buƙaci jami'an da su miƙa musu waɗanda ake zargin domin su kashe su da kansu, lamarin da ya jawo rigima ta barke a cikin ofishin.

Kashe mutane 3 da jikkata jami'an tsaro

Duk da ƙoƙarin jami’an na kwantar da hankalin jama’a, mutanen sun yi amfani da ƙarfi inda suka kutsa cikin ofishin tare da balle kofofin ginin.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kai kazamin hari a Kebbi

Kafin wasu jami’an tsaro su kai dauki wurin, fusatattun mutanen sun cinna wa ofishin wuta sannan suka kwashe waɗanda ake zargin suka kashe su ta hanyar duka.

Yayin da jami’an NSCDC da ke bakin aiki suka sami nasarar tserewa daga ofishin da ke cin wuta, uku daga cikinsu sun sami raunuka daban-daban kuma suna karɓar magani a halin yanzu.

Hukumar NSCDC ta fara binciken hargitsin da aka yi a Dawakin Kudu na jihar Kano inda aka kashe mutane da kona ofishinta.
Taswirar jihar Kano, inda aka kona ofishin NSCDC tare da kashe mutane 3. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kafa kwamitin binciken harin NSCDC

Kwamandan rundunar na jihar Kano, Mohammed Agalama, ya kafa wani kwamiti na musamman domin gudanar da bincike mai zurfi kan wannan hari.

Rundunar ta yi kira ga al'ummar Dawakin Kudu da su kwantar da hankulansu tare da guje wa ɗaukar doka a hannunsu.

Ibrahim Abdullahi ya jaddada cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa wajen gano waɗanda suka jagoranci ƙona ofishin da kuma kisan gillar da aka yi domin fuskantar shari’a.

NSCDC: An kashe mutane 3 a Katsina

A wani labari, mun ruwaito cewa, harsasai da suka fita daga cikin bindigar 'yan sanda sun yi ajalin mutane biyu a Katsina, bayan afkuwar wata hatsaniya.

Rikici ya barke tsakanin jami'an tsaro da mutanen gari ne lokacin da aka je kama wani matashi mai suna Kuda a Sabuwar Unguwa.

Rahoton 'yan sanda ya yi bayani dalla dalla kan yadda fusatattu suka kona ofishin NSCDC da kuma yadda mutuwar matasan ta kasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com