Akwai Matsala: ’Yan Bindiga Sun Dabawa Malaman Addini 2 Wuke kusa da Abuja

Akwai Matsala: ’Yan Bindiga Sun Dabawa Malaman Addini 2 Wuke kusa da Abuja

  • Ana fargabar wasu 'yan bindiga sun kai hari kan malaman addini guda biyu mabiya darikar Katolika a Mararaba da ke jihar Nasarawa
  • Lamarin ya faru ne a kusa da birnin Abuja, inda suka daba musu wuka da dare abin da ya tayar da hankulan al'umma
  • Fastocin sun samu munanan raunuka, amma an kai su asibiti cikin gaggawa kuma an ce yanayin lafiyarsu ya daidaita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – ’Yan bindiga sun kai mummunan hari kan Fastocin Katolika biyu a gidansu da ke Cocin St. Rita Katolika a Mararaba da ke Jihar Nasarawa.

An ce lamarin ya faru ne kusa da Abuja, abin da ya sake tayar da hankula kan tabarbarewar tsaro a yankin Babban Birnin Tarayya.

An dabawa Fastoci 2 wuka a kusa da Abuja
Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun da kofar shiga cocin katolika. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Yan bindiga sun farmaki Fastoci da wuka

Kara karanta wannan

'Don Allah ka zauna a Kiristanci': Rokon matar Sanata Akume bayan ya kara aure

Rahoton Vanguard ya nuna cewa harin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na dare, lokacin da wasu ’yan bindiga dauke da makamai suka kutsa cikin gidan da karfi.

An ce sun daba musu wuka, suka bar su kwance cikin jini, yayin da babban Faston cocin ya tsira da ransa ba tare da rauni ba.

An bayyana sunayen wadanda aka kai wa harin da Fasto Comas Baye da ke zaune a cocin da kuma Fasto Chris Pever.

Rahotanni sun ce Fasto Baye ya gamu da shanyewar bangaren jikinsa sakamakon harin yan bindiga.

An garzaya da Fastocin biyu zuwa asibitin katolika na Nativity da ke Jikwoyi, Abuja, inda ake basu kulawar gaggawa.

An ce Fasto Pever ya samu mummunan rauni ciki har da karyewar hannun hagu, inda aka yi masa tiyata tare da saka masa wani na’ura na musamman.

An yi Allah-wadai da hari kan Fastoci a Najeriya
Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Martanin cocin kan mummunan lamarin a Nasarawa

Kungiyar Abuja Grand Commandery ta cocin ta yi Allah-wadai da harin, tana mai bayyana shi a matsayin mugun hari kan limaman addini da ba su san komai ba , tare da nuna damuwa kan karuwar rashin tsaro a Abuja da jihohi makwabta.

Kara karanta wannan

'Ba mu bukatar taimakon azzalumai': Gumi ya soki Amurka kan hari a Sokoto

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar, Birgediya-janar Francis Ulonna Njoku, da Sakataren Kungiyar, Kanal Etta Peters sanyawa hannu.

Kungiyar ta ce harin ba abu ne da ya faru haka kawai ba, illa wani bangare ne na yawaitar hare-hare kan wuraren ibada da malaman addini a Abuja jihohin da ke makwabtaka da ita.

Sanarwar ta ce:

“Wannan mummunan hari ba wai kai wa Fastoci kawai ba ne, illa tozarta darajar rayuwar dan Adam, cibiyoyin addini da kuma ginshikin tarbiyyar al’umma wanda ke jawo matsaloli."

Matashi ya kashe mutane 3 a masallaci

An ji cewa wani matashi da ake zargi ya sha miyagun kwayoyi, ya kashe mutane uku a lokacin sallar Asubahi a wani masallaci a Abuja.

Rahotanni daga shaidun gani da ido sun nuna cewa matashin mai suna, Laminde Boka ya kashe mutanen ana dab da fara sallah a Gwarimpa.

Mutane sun yi kokarin kama wanda ake zargin, kuma sun lakada masana na-jaki har ya mutu a kusa da masallacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.