'Yan Bindiga Sun Gudo daga Sakkwato bayan Harin Amurka, Sun Fada Tarkon Amotekun

'Yan Bindiga Sun Gudo daga Sakkwato bayan Harin Amurka, Sun Fada Tarkon Amotekun

  • Jami'an rundunar Amotekun ta jihar Ondo sun kama wasu da ake zargin yan bindiga k'ne da suka gudo daga farmakin da Amurka ta kai Sakkwato
  • Babban kwamandan Amotekun, Adetunji Adeleye ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Akure
  • Ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa daga yankin Sakkwato suka tsere, amma ya ba da tabbacin cewa za a gudanar da sahihin bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo, Nigeria - Jami’an rundunar tsaron jihar Ondo, wadda aka fi sani da Amotekun, sun kama mutane 39 da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka gudo daga jihar Sakkwato.

Ana zargin yan ta'addan sun tsero daga Jihar Sakkwato ne bayan hare-haren sama da Amurka ta kai kan ‘yan bindiga masu alaka da kungiyar IS a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kai kazamin hari a Kebbi

Dakarun rundunar Amotekun.
Dakarun rundunar tsaro ta jihar Ondo, Amotekun Hoto: Amotekun Corps
Source: Twitter

Kwamandan rundunar Amotekun na Jihar Ondo, Adetunji Adeleye, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Akure, kamar yadda The Nation ta ruywaito.

An kama 'yan bindiga a jihar Ondo

Kwamandan ya gabatar da mutane 61 da dakarun Amotekun suka kama a sassa daban-daban na jihar Ondo, a yayin sintirin tsaro na Ember da ake gudanarwa.

A cewar Adeleye, mutane 39 daga cikin wadanda aka kama sun yi bayani a lokacin bincike cewa sun gudo ne daga Jihar Sakkwato bayan luguden wutan da sojoji suka yi masu.

“Wadannan mutane 39 da muka kama da kansu suka fada mana ce 'wa sun tsere ne daga yankin Sakkwato,” in ji shi.

Ya ce a halin yanzu suna ci gaba da binciken mutanen, da aka gano ba su wuce shekaru tsakanin 18 zuwa 45, wadanda ake zargin 'yan bindiga ne.

Kwamandan Amotekun ya tabbatar da cewa duk wanda aka kama da hujjojin da ke nuna yana da laifi, za a gurfanar da shi gaban kotu.

Kara karanta wannan

Mutane sun ga jirage na shawagi, sun fara guduwa saboda tsoron harin Amurka

Nasarorin dakarun Amotekun a jihar Ondo

Mista Adeleye ya kara bayyana cewa Amotekun ta kara kaimi wajen sintiri da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, musamman a iyakar kananan hukumomi da ke hada Jihar Ondo da Ekiti, Osun, Ogun, Edo da Kwara.

Yayin da yake bayani dalla-dalla, kwamandan ya ce daga cikin mutane 61 da dakarun tsaro suka kama, 50 sun shiga hannu ne saboda zargin yunkurin tada zaune tsaye.

Dakarun rundunar Amotekun.
Jami'an rundunan tsaro ta Amotekun a bakin ofishinsu na jihar Ondo Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Source: Facebook

Sai kuma masu garkuwa da mutane shida, biyu bisa laifin karya dokar kiwon dabbobi da kuma wasu mutum uku da aka kama kan laifin cin zarafin mata.

Ya danganta nasarar da aka samu ga jajircewa da hadin kai na jami’ai da ma’aikatan Amotekun wajen kawar da masu aikata laifuffuka a fadin jihar Ondo, cewar Leadership.

An kama mai garkuwa da mutane a Ondo

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ’yan sandan jihar Ondo ta kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane, Godspower Cletus lokacin da ya je cire kudi a PoS.

Kara karanta wannan

Majiyoyi sun fadi ranar da Gwamnan Kano, Abba zai sanar da komawa APC

Rahotanni sun ce an kama shi ne a wani shagon POS bayan ya yi wa wata mata barazana tare da karɓe wayarta da katin bankinta na ATM.

Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin gano ko akwai wasu da ke taimaka masa a aikata laifuffukan garkuwa da mutane a jihar

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262