‘Don Allah Ka Zauna a Kiristanci’: Rokon Matar Sanata Akume bayan Ya Kara Aure

‘Don Allah Ka Zauna a Kiristanci’: Rokon Matar Sanata Akume bayan Ya Kara Aure

  • ‘Yar majalisa mai wakiltar mazabar Gboko/Tarka, Regina Akume, ta ba mijinta sakataren gwamnatin tarayya shawara
  • Regina ta shawarci mijin nata da ya dawo cikakken tafarkin addinin Kiristanci ganin ya kara aure a cikin makon da ya gabata
  • Ta ce duk nasarorin da Akume ya samu a rayuwa sun samo asali ne daga imaninsa na Kiristanci da darajar Yesu Almasihu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Jihar Benue – ‘Yar majalisar tarayya mai wakiltar Gboko/Tarka, Regina Akume, ta roki mijinta, Sakataren Gwamnatin Tarayya kan rike addini.

Regina ta roki George Akume, da kada ya yi watsi da addinin Kiristanci, tana mai jaddada cewa dukkan nasarorin da ya samu a rayuwa sun samo asali ne daga imaninsa na Kirista.

Matar Akume ta roke shi ya zauna a Kiristanci
Yar majalisar tarayya, Regina Akume da Sanata George Akume da amaryarsa Sarauniya Zaynab. Hoto: Hoto: Authenticvoice6.
Source: Twitter

Rokon da matar Akume ta yi gare shi

Matar Akume ta yi wannan kira ne a cikin wani bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta, wanda gidan talabijin na Idoma ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Biki Bidiri: An daura auren Zaynab da sakataren gwamnatin tarayya a asirce

An dauki bidiyon ne yayin liyafar bikin aure da aka gudanar a Makurdi a Jihar Benue.

Hakan ya zo ne kwanaki kadan bayan tsohon Sanatan na Arewa maso yammacin Benuwai ya cika shekaru 72 a duniya.

A yayin addu’ar ranar haihuwa da ta yi masa, Regina Akume ta roki Allah da ya ba mijinta tsawon rai, cikakkiyar lafiya da hikima, tare da tunatar da shi muhimmancin tushen imaninsa na Kirista.

Ta ce:

“Ina addu’a Allah ya kara masa shekaru, ya ba shi lafiyar jiki da kwakwalwa, ya ba shi karfin kwakwalwa wajen tunani da yin abin da ya dace.”

Ta kara da cewa addinin Kiristanci ne ya taka muhimmiyar rawa wajen kai mijinta matsayinsa a yanzu, tana mai gargadin cewa barin addinin zai iya kawo masa koma baya.

Ta ce:

“Ya kamata ya tuna cewa shi Kirista ne, kuma Kiristanci ne ya kai shi wannan matsayi. Idan ya bar Kiristanci yanzu ya bi wani abu daban, ba zai yi nasara ba.
“Don haka shawarata gare shi ita ce ya dawo Kiristanci, ya bi tafarkin Almasihu.”

Kara karanta wannan

Yahaya Bello zai nemi kwace kujerar Sanata Natasha a zaben 2027

Matar Akume ta ba shi shawara kan Kiristanci
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume. Hoto: Authenticvoice6.
Source: Twitter

Regina ta fadawa Akume gaskiya kan rayuwarsa

Regina ta ce ya kai wannan matsayi na SGF ba ta wata hanya ba sai ta wurin Yesu Almasihu kuma yana raye har yanzu yana aiki, yana yi musu alheri, ta ce tana fatan zai dawo Kiristanci.

Wadannan kalamai sun zo ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan rahoton cewa Sanata Akume ya auri wata mata ta biyu, cewar Punch.

Baya ga mukamin da yake kai a yau, Akume ya rike minista a zamanin Muhammadu Buhari kuma ya je majalisar dattawa bayan ya yi gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan ya auri wata mace daga gidan sarauta wadda aka gabatar da ita a matsayin Sarauniya Zaynab Ngohemba-George Akume Dajoh.

Zaynab ita ce tsohuwar matar babban basarake a kasar Yarbawa watau Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi.

2027: Akuma ya ba Atiku, El-Rufai shawara

Mun ba ku labarin cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ya bukaci Atiku Abubakar da sauran ƴan siyasa su mutunta tsarin karɓa-karɓa a 2027.

Kara karanta wannan

'Ba mu bukatar taimakon azzalumai': Gumi ya soki Amurka kan hari a Sokoto

Sanata Akume ya ce bai kamata manyan ƴan siyasar Arewa su nemi karɓar mulki a 2027 ba saboda Bola Tinubu da yankin Kudu ba su cinye wa'adinsu ba.

Ya ce tun da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas, ya kamata a bar Kudu ta yi shekaru takwas kafin mulki ya dawo Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.