JED Ya Nemi Masallatai da Coci Su Rika Biyan Kudin Lantarki a Jihar Gombe
- Kamfanin rarraba wutar lantarki na JED ya bayyana damuwa kan yadda wasu masallatai, coci-coci da masu injin niƙa ke ƙin amincewa da karbar mita
- Rahoto ya nuna cewa JED ya ce matakin na haddasa asarar kuɗi masu yawa, tare da kawo cikas ga tsarin biyan kuɗin wuta cikin gaskiya da adalci
- Kamfanin ya yi kira ga shugabannin addinai da ’yan kasuwa da su goyi bayan tsarin saka mita domin inganta sahihanci da dorewar samar da wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Kamfanin rarraba wutar lantarki na JED ya bayyana cewa ana ci gaba da fuskantar ƙalubale a Jihar Gombe sakamakon ƙin amincewar wasu masallatai, coci-coci da masu injin niƙa kan kafa musu mita.
Kamfanin ya bayyana cewa wannan matsala na ƙaruwa ne musamman bayan da batun ya fara yawo a shafukan sada zumunta, inda wasu ke nuna adawa da tsarin, lamarin da kamfanin ke ganin ba ya amfani ga kowa.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa hakan na janyo babbar asarar kuɗin shiga tare da kawo barazana ga dorewar rarraba wutar lantarki a yankin.
Korafin JED ga masallatai da coci
Shugaban sashen kula da ayyukan kamfanin JED, Musa Abdullahi, ya ce abin mamaki ne yadda cibiyoyin addini ke ƙin amincewa da na’urar da aka tsara domin auna yawan wutar da ake amfani da ita.
Ya bayyana cewa addini na koyar da gaskiya da kyautata hali, tare da hana satar dukiya, don haka ya ce bai dace a ƙi tsarin da ke tabbatar da biyan abin da aka yi amfani da shi ba.

Source: Facebook
A cewarsa, mitar da ake saka wa hanya ce ta tabbatar da adalci, domin tana nuna ainihin yawan wutar da mai amfani ke kashewa ba tare da ƙari ko ƙorafi ba.
Matsayar JED kan masallaci da coci
Abdullahi ya jaddada cewa kamfanin rarraba wuta ba ya bambance mai amfani da wuta bisa addini ko sana’a. Ya ce a tsarin kamfani, kowa mai amfani da wuta ana kallonsa a matsayin abokin ciniki.
Ya ƙara da cewa wuta ba ta san masallaci, coci ba, illa dai tana aiki ne bisa amfani da ake yi da ita. Saboda haka, duk wanda ke amfani da wuta ya dace ya bi ƙa’idojin biyan kuɗin da aka tanada.
Kamfanin ya bayyana cewa cibiyoyin ibada na cikin rukunin masu amfani da wuta mai yawa, saboda kayan lantarki da ake amfani da su a lokacin ibada da taruka.
JED na asarar kudin shiga a Gombe
Kamfanin ya bayyana cewa akwai gibi mai yawa tsakanin wutar da ake rabawa da kuɗin da ake karɓa a kowane wata. A wasu watanni, asarar na kai daruruwan miliyoyin Naira.
Ya bayyana cewa duk da samun wuta mai yawa daga cibiyar samarwa, kuɗin da ake tarawa bai kai rabin abin da ya dace ba, lamarin da ke jefa kamfanin cikin matsin tattalin arziki.
Alal misali a watan Satumban 2025, kamfanin ya ce ya saye wutar N1.67bn, amma N757m kawai ya iya karba a matsayin kudin lantarki, ya ce ya yi asarar N800m.
A karshe, kamfanin ya yi kira ga limamai, fastoci da shugabannin al’umma da su ƙarfafa mambobinsu su amince da saka musu mita.
Ana gyara lantarkin Najeriya inji minista
A wani labarin, kun ji cewa ministan makamashin Najeriya, Bayo Adelabu ya bayyana cewa na kusa kammala gyaran wuta da ake yi.
Adelabu ya bayyana haka ne yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a birnin tarayya Abuja, inda suka tattauna inganta makamashi.
A bayanan da ya yi, ministan ya ce an samu wata matsala ce da ke da alaka da bututun gas, kuma ana shirin magance damuwar.
Asali: Legit.ng


