Ta Faru Ta Kare: EFCC Ta Gurfanar da Malami da 'Dansa a Gaban Babbar Kotun Tarayya

Ta Faru Ta Kare: EFCC Ta Gurfanar da Malami da 'Dansa a Gaban Babbar Kotun Tarayya

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN), dansa da wani mutum daya kan zargin safarar kudi ta hanyar haram
  • Rahotanni sun nuna cewa duk wadanda ake tuhuma sun musanta aikata kowane laifi a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja
  • EFCC ta tuhumi Malami da sauran abokan hadin gwiwarsa da karkatar da biliyoyin Naira ta haramtacciyar hanya tare da sayen kadarori da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN) a gaban kotu.

Hukumar EFFC ta gurfanar da Malami ne kan wasu tuhume-tuhume da take masa da suka shafi almundahana da sama da fadi da dukiyar kasa.

Abubakar Malami.
Tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN) Hoto: Abubakar Malami
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa an gurfanar da Malami a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata tare da ɗansa, Abubakar Abdulaziz Malami da wata Bashir Asabe, kan tuhume-tuhume 16.

Kara karanta wannan

Malami: Kotu ta iza ƙeyar surukin Buhari da ɗansa zuwa gidan yarin Kuje

Tuhume-tuhumen sun haɗa da halatta kudaden haram da kuma mallakar kadarorin da suka kai sama da Naira biliyan 8.7 ba bisa ƙa'ida ba.

Malami ya musanta tuhumar da ake masa

Duka waɗanda ake tuhuma, Malami, dansa da Bashir Asabe sun ƙi amsa laifuffukan da ake zarginsu da su ba a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite.

A cikin takardar tuhuma mai lamba FHC/ABJ/CR/700/2025, gwamnatin tarayya ta zargi Malami da ɗansa cewa sun yi amfani da wani kamfani domin boye kudaden haram da suka sata.

Ta shaida wa alkali cewa a tsakanin Yulin 2022 zuwa Yunin 2025, sun yi amfani da kamfanin Metropolitan Auto Tech Limited domin ɓoye haramtattun kuɗi da ya kai Naira 1,014,848,500.

Haka kuma, gwamnatin ta ce Malami ya yi amfani da kamfanin wajen ɓoye kuɗi har Naira 600,013,460.40 a cikin asusun Sterling Bank Plc mai lamba 0079182387.

EFCC ta zargi Malami da sayen kadarori

EFCC ta ƙara zargin cewa Malami ya yi amfani da kuɗin haram da suka kai Naira miliyan 952 wajen mallakar gidaje da yawa a Abuja, Kano, da Birnin Kebbi tsakanin 2018 da 2023.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: An maka Wike da gwamnoni 36 a kotu kan Naira tiriliyan 14

Hukumar EFCC ta lissafa shaidu da dama, ciki har da masu bincike, jami'an banki, masu canjin kuɗi, da wakilan kamfanoni, don gamsar da kotu a shari'ar.

Abubakar Malami.
Tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami
Source: Facebook

Ta ce laifuffukan da ake zargin Malami da sauran mutane biyu sun saba wa Dokar Hana Safarar Kuɗi ta 2011, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

EFCC ta gano wasu kadarorin Malami

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta gano wasu kadarori fiye da 40 da ake zargin suna da alaka da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami.

Kadarorin sun haɗa da otal-otal, gidajen zama na alfarma, filaye, makarantu da kamfanin ɗab'i, kuma suna a jihohin Kebbi, Kano da birnin Abuja.

Kadarorin da ke Kebbi sun kai darajar N162,195,950,000, na Kano sun kai N16,011,800,000, yayin da kadarorin da ke Abuja suka kai darajar N34,685,000,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262