'Makaman da Amurka Ta Harbo Najeriya Sun Kara Tona Asirin Gwamnatin Bola Tinubu'

'Makaman da Amurka Ta Harbo Najeriya Sun Kara Tona Asirin Gwamnatin Bola Tinubu'

  • Gbenga Olawepo Hashim ya yi fatali da hare-haren da Amurka ta kai kan yan ta'adda a jihohin Sakkwato da Kwara domin taimakawa Najeriya
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce wadannan hare-haren na kasar Amurka sun fallasa irin gazawar da gwamnatin APC ta yi
  • Ya ce duk da ba ya adawa da tasirin taimakon kasashen waje amma mafitar da aka samar a cikin gida ce za ta magance matsalar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon 'dan takarar shugaban ƙasa, Gbenga Olawepo Hashim, ya soki hare-haren sama da Amurka ta kai kan ’yan ƙungiyar Islamic State (IS) a Najeriya.

Ya bayyana matakin a matsayin wata babbar shaida da ta fallasa gazawar tsarin tsaron ƙasar a ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin APC.

Kara karanta wannan

Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

Gbenga Olawepo Hashim.
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jigo a PDP, Gbenga Olawepo Hashim
Source: Facebook

Gbenga Olawepo Hashim ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.

Hashim ya soki hare-haren Amurka

Hashim ya ce hare-haren na Amurka sun nuna yadda ƙasashen waje ke ƙara nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, musamman a yankin Arewa maso Yamma, inda ƙungiyoyin ta’addanci ke ƙara mamaye wa.

Ya kara da cewa tun daga shekarar 2021 tawagarsa ke jan hankalin gwamnati kan cewa yanayin tsaro a Arewa maso Yamma na nuna hatsarin da ke tafe, amma ta yi kunnen uwar shegu.

'Dan siyasar, wanda ke da burin sake neman shugabancin Najeriya, ya ce sun dade da nuna wa gwamnati yiwuwar bullar 'yan ta'adda da ke da alaƙa da IS, idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Abubuwan da ke rura wutar matsalar tsaro

Ya danganta tabarbarewar tsaron da ƙaruwar talauci, gazawar shugabanci, da raunin hukumomi, wanda a cewarsa ya ƙarfafa ƙungiyoyin 'yan ta'adda masu tsattsauran ra’ayi.

Kara karanta wannan

Martanin Tambuwal da sauran manyan 'yan siyasa kan harin Amurka a Najeriya

“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne nada mutane da ke taimakawa ko ke neman kare tsattsauran ra’ayi a manyan mukaman siyasa, wanda hakan ya ba ƙungiyoyin yan ta’adda damar kwace yankuna,” in ji Hashim.
Shugaba Tinubu, Gbenha Hashim.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Gbenga Olawepo Hashim Hoto: @Hashimtalks
Source: Twitter

Duk da ya amince hare-haren ƙasashen waje kamar Amurka na iya rage ƙarfin ’yan ta’adda na ɗan lokaci, Gbenga Hashim ya jaddada cewa a cikin Najeriya ne kadai za a samu mafita mai ɗorewa.

“Yanayin tsaro a Arewa maso Yamma ya yi muni matuƙa. Ba tare da daukar matakin cikin gida da kyakkyawan shugabanci ba, dauki daga sojojin kasashen waje ba zai haifar da sakamako mai ɗorewa ba,” in ji shi.

Hashim ya nuna shakku kan ko gwamnatin APC ta shirya aiwatar da muhimman gyare-gyaren cikin gida, a cewarsa matsalolin shugabanci da tsaro nd ke barazana ga makomar dimokuraɗiyyar Najeriya, cewar Vanguard.

Mutanen Borno sun tsorata da harin Amurka

A wani labarin, kun ji cewa mutane sun fara ganin jiragen sama na shawagi a wasu yankuna a jihar Borno kwanaki kadan bayan farmakin da Amurka ta kawo Najeriya.

Hakan ya sa wasu mazauna ƙauyuka a Jihar Borno ke tunanin barin muhallansu zuwa wurare mafi aminci, sakamakon yiwuwar kai hare- haren bama-bamai daga sojojin Amurka.

Wani mazaunin yankin, Abba Dankale, ya ce hare-haren sama da Amurka ta kai a Jihar Sokkwato a Arewa maso Yammacin Najeriya, sun tsoratar da su matuƙa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262