Akpabio: Kungiya Ta Bankado Makarkashiyar da Ake Kullawa Shugaban Majalisar Dattawa

Akpabio: Kungiya Ta Bankado Makarkashiyar da Ake Kullawa Shugaban Majalisar Dattawa

  • An sake taso da batun yunkurin tsige shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio daga mukaminsa
  • Wata kungiiya ta fito ta yi zargin cewa akwai wani shiri da ake yi na ganin an raba Akpabio da kujerar shugabancin majalisar dattawa
  • NGM ta gargadi masu wannan shirin da su guji kawo abin da zai wargaza zaman lafiya a majalisar dattawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wata kungiya mai suna National Grassroots Movement (NGM) ta yi zargin an shirya wata makarkashiya kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Kungiyar ta yi zargin cewa wasu sanatocin Arewa sun tsara shiri mai kyau domin tsige Godswill Akpabio.

An fallasa shirin tsige Akpabio a majalisar dattawa
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran kungiyar na kasa, Tunde Felix da sakataren yada labarai, Alhaji Musa Mustapha suka fitar a ranar Litinin, 29 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Bayan harin Amurka, Akpabio ya fadi lokacin kawo karshen matsalar rashin tsaro

Batun tsige Godswill Akpabio

Zargin na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya fito ya musanta rahotannin da ke cewa ana shirin tsige Akpabio.

Shugaban masu rinjayen ya ce labaran ba su da tushe kuma an kirkire su ne da gangan domin haddasa rarrabuwar kawuna a majalisar, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

Bamidele ya yi wannan martani ne kan kalaman Sanata Orji Kalu (Abia ta Arewa), wanda ya ce akwai yunkurin da wasu sanatoci suka yi na tsige Akpabio amma bai yi nasara ba.

Wane zargi kungiyar NGM ta yi?

Sai dai kungiyar NGM ta yi Allah-wadai da abin da ta kira shirin tsige Akpabio, wanda ta ce yana yin jagoranci mai kyau a majalisar dattawan ta 10.

A cewar kungiyar, salon hadin kan Akpabio da bangaren zartarwa ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingantaccen mulki a lokacin da Najeriya ke bukatar tsari, hadin kai da daukar matakai masu karfi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi bayani kan harin bam da ya kashe Musulmai a masallacin Borno

"Kungiyar National Grassroots Movement na fallasa wani kulli na siyasa da ke nuna wani tsari mai kyau da aka tsara daga wani bangare na sanatocin Arewa domin tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, saboda muradin kansu.”
“Wannan shiri ba ya da alaka da ka’ida, gyara ko ci gaban majalisa, illa kawai yunkuri ne na kwace iko".

- Tunde Felix

Kungiya ta ce sanatocin Arewa na shirin tsige Akpabio
Sanata Godswill Akpabio a zauren majalisar dattawa Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Kungiyar NGM ta yi gargadi

Kungiyar ta amince cewa sauyin shugabanci a majalisa halas ne a karkashin kundin tsarin mulkin mulkin Najerya.

Amma ta ce kirkirar irin wadannan sauye-sauye ta hanyar nuna bangaranci, maimakon muradin kasa baki daya, na haifar da tambayoyi masu zurfi tare da barazana ga kwanciyar hankalin majalisa.

Yayin da take yin Allah-wadai da duk wani yunkuri na amfani da kabilanci, addini ko rinjayen yawa wajen kwace shugabancin majalisar dattawa, kungiyar ta gargadi masu hannu a ciki da kada su maida majalisar fagen ramuwar gayya ta kashin kai.

Ayarin motocin Akpabio sun gamu da hatsari

A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar ayarin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya gamu da hatsari a jihar Oyo.

Lamarin ya yi sanadiyyar rasuwar wani jami’i da ke tare da tawagar da ake kiransu ‘Dispatch riders’ mai suna Ibrahim Hussaini

Shugaban majalisar dattawan ya jajanta wa iyalan marigayin bisa babban rashin da suka yi sakamakon hatsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng