Ana Jita Jitar Zai Koma APC, Majalisa Ta Yi Wa Gwamna Abba Kari a Kasafin Kudin 2026
- Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kasafin kudin shekarar 2026, wanda zai lakume fiye da Naira tiriliyan 1.4
- Hakan dai ya biyo bayan kammala karatu na uku kan kudirin kasafin da Majalisar ta yi a zamanta na yau Litinin, 29 ga watan Disamba, 2025
- Shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin Kano, Hon. Husseini Lawan ya ce an samu karin sama da Naira biliyan 100 a kasafin kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kasafin kuɗi na shekarar 2026 da ya kai Naira tiriliyan 1.47
Hakan dai na nufin Majalisar dokokin ta ƙara Naira biliyan 109.7 kan adadin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar tun da farko.

Source: Facebook
Majalisar dokokin Kano ta amince da kasafin 2026
Leadership ta rahoto cewa an amince da kasafin kuɗin, wanda jimillarsa ta kai N1,477,829,666,131, a zaman Majalisar Kano na ranar Litinin, 29 ga watan Disamba, 2025.

Kara karanta wannan
Kasafin 2026: Gwamna ya ware Naira biliyan 12 don samar da tsaro a Arewacin Najeriya
Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Ismail Falgore, shi ne ya jagoranci zaman a daidai lokacin da ake rade-radin Gwamna Abba zai sauya sheka daga NNPP zuwa APC.
Majalisa ta amince da kundin ne bayan kammala nazari kan kudirin kasafin da gwamnan Kano ya gabatar, tare da yi wa kasafin kudin karatu na uku wanda shi ne na karshe a doka.
Tun da farko, Gwamna Abba ya gabatar da kasafin kuɗi na N1,368,127,929,271, wnada ya yi wa taken “Budget of Infrastructure, Inclusive Growth and Sustainable Development."
Majalisar jihar Kano ta yi kari a kasafin 2026
Da yake zantawa da ’yan jarida, Shugaban Masu Rinjar Majalisa, Husseini Lawan, ya ce an ƙara kasafin kuɗin ne sakamakon hasashen samun ƙarin kuɗaɗen shiga, musamman daga asusun tarayya da harajin VAT.
Ya bayyana cewa kasafin ya ƙunshi Naira tiriliyan 1.048 na ayyukan more rayuwa wanda ke wakiltar kusan kashi 75 cikin 100 na jimillar kasafin kudin 2026.
Haka zalika an ware Naira biliyan 429 domin kashen kuɗaɗen yau da kullum na gudanar da harkokin gwamnati, wato kashi 25 cikin 100, cewar rahoton Tribune.
Bangarorin da gwamnatin Kano ta ba fifiko
A cewar Hon. Lawan, bangarorin ilimi da lafiya sun samu kaso mafi yawa, abin da ke nuna fifikon da Majalisar ta bai wa abubuwan da suka shafi inganta rayuwar dan adam.
Bangaren ilimi ya samu kusan kashi 30 cikin 100 na kasafin Kano gaba ɗaya, wanda ya haura ka’idar UNESCO, yayin da bangaren lafiya ya samu kashi 16 cikin 100.
Husseini Lawan ya ce an ƙara kasafin ilimi da Naira biliyan 19, daga Naira biliyan 405 da gwamna ya gabatar zuwa kusan Naira biliyan 425, yayin da bangaren lafiya ma ya samu ƙarin Naira biliyan 2.59.

Source: Facebook
A farkon zaman, Majalisar ta yi shitun mintu guda domin karrama ’yan majalisa biyu—Aminu Sa’ad (Ungogo) da Sarki Aliyu Danaji (Kano Municipal), waɗanda suka rasu a ranar 24 ga Disamba, 2025.
Gwamna Abba na shirin komawa APC
A wani labarin, kun ji cewa jita-jitar sauya sheƙar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na dab da zama gaskiya bayan jawabin jam'iyyarsa ta NNPP.
Wata majiya ta yi ikirarin cewa gwamnan Kano na iya bayyana matsayinsa a fili a yayin taron majalisar zartarwar jihar da ake sa ran za a gudanar nan kusa.
Duk da karfin labarin sauya shekar Gwamnan Kano, har yanzu Abba Kabir Yusuf bai ce komai ba, amma makusantansa suna maganar cewa za su iya sauya sheka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

