Kasafin 2026: Gwamna Ya Ware Naira Biliyan 12 don Samar da Tsaro a Arewacin Najeriya
- Gwamna Inuwa Yahaya ya sanya hannu kan kasafin jihar Gombe na 2026 da ya kai Naira biliyan 617 domin gudanar da ayyukan raya kasa
- Jihar Gombe za ta rinka bayar da gudunmawar Naira biliyan daya a kowane wata domin tallafawa asusun tsaro na jihohin Arewacin Najeriya
- Kasafin kudin ya fi mayar da hankali kan manyan ayyukan raya kasa, fannin ilimi, lafiya, da kuma samar da tsaro mai dorewa a jihar Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Gwamna Inuwa Yahaya ta ta ɗauki matakin gaba-gaba a fafutukar yaƙi da rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ware Naira biliyan 12, wanda zai sanya a asusun tsaro na shiyya a kasafin kuɗinta na shekarar 2026.

Kara karanta wannan
Ana jita jitar zai koma APC, Majalisa ta yi wa Gwamna Abba kari a kasafin kudin 2026

Source: Twitter
Gwamna ya ware N12bn don tsaron Arewa
Mai girma gwamna ya sanya wa dokar kasafin kuɗin ta shekarar 2026 da aka kiyasta za a kashe Naira biliyan 617.95 hannu a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
Babban abin lura a wannan kasafi shi ne tanadin Naira biliyan 12 don asusun tsaron Arewa, wanda hakan ke nufin gudunmawar Naira biliyan ɗaya a kowane wata.
Wannan kuwa ya yi daidai da yarjejeniyar da ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa ta cimma, ta kowace gwamna ya sanya tallafin Naira biliyan daya duk wata don magance matsalar tsaro.
Gwamna Inuwa ya jaddada cewa tsaro ne silar kowane irin ci gaba da bunƙasar tattalin arziki, don haka jihar Gombe za ta ci gaba da ba da muhimmanci wajen kare rayuka da dukiyar al'umma ta hanyar samar da isassun kudade.
Gombe: Muhimman bangarorin kasafin 2026
Baya ga fannin tsaro, kasafin kuɗin ya samar da Naira biliyan 189 domin manyan ayyukan yau da kullum yayin da aka ware kashi 69.4 cikin ɗari na kasafin, wato Naira biliyan 428.5, domin manyan ayyukan raya ƙasa.
Wannan na nuna yadda gwamnatin jihar ta mayar da hankali kan samar da ababen more rayuwa, inganta ilimi, lafiya, da kuma kare muhalli.
Haka kuma, Gwamna Inuwa Yahaya ya yi tanadi na musamman ga hukumar kula da naƙasassu ta jihar Gombe, kamar yadda rahoto ya nuna.

Source: Original
Majalisa ta kara yawan kudin kasafin 2026
Tun farko, gwamnan ya gabatar da kasafin Naira biliyan 535.69 ga majalisar dokokin jihar, amma bayan bincike da nazari, majalisar ta ƙara sama da Naira biliyan 82, wanda ya kai jimillar kasafin zuwa Naira biliyan 617.95.
Gwamna Yahaya ya yaba wa majalisar dokokin jihar bisa jajircewarsu wajen duba kasafin da kuma goyon bayan da shugaba Bola Tinubu ke ba wa jihar.
Ya kuma ba al'umma jihar Gombe tabbacin cewa za a aiwatar da kasafin ta yadda zai taɓa rayuwar mazauna birane da karkara baki ɗaya.
Gwamnonin Arewa sun kafa asusun tsaro
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnonin Arewa sun cimma matsaya a kan batutuwa daban-daban da suka danganci tsaron yankin tare da nema wa kansu mafita.
A wani muhimmin taro da gwamnoni, sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsakin suka gudanar a yankin, an amince da samar da asusun tsaro na yaki da 'yan ta'adda.
Gwamnonin sun sake nanata goyon bayansu ga ‘yan sandan jihohi domin karfafa tsaro da kawo karshen kashe-kashen da ake yi wa al'umomin wannan yanki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

