Mutane Sun Ga Jirage na Shawagi, Sun Fara Guduwa saboda Tsoron Harin Amurka
- An fara ganin jiragen sama na shawagi a wasu yankuna a jihar Borno kwanaki kadan bayan farmakin da Amurka ta kawo Najeriya
- Wasu mazauna kauyuka a Borno sun fara gudun hijira zuwa wurare masu tsaro saboda fargabar yiwuwar Amurka ta kaddamar da hari
- Wani da ya nemi a sakaya sunansa ba ya bayyana cewa manoma a Dawashi, Malam Karanti da wasu kauyuka sun fara ƙaura zuwa garin Baga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Wasu mazauna ƙauyuka a Jihar Borno na tunanin barin muhallansu zuwa wurare mafi aminci, sakamakon yiwuwar kai hare-haren bama-bamai daga sojojin Amurka.
A cewar wasu daga cikinsu, sun hangi jiragen yaƙin sojoji suna shawagi a sama na kusan mintuna 30 a ranar Lahadin da ta gabata kafin daga bisani su ɓace.

Kara karanta wannan
Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

Source: Original
Wannan al'amari na zuwa ne bayan harin da sojojin Amurka suka kai jihohin Sakkwato da Kwara da nufin kakkabe 'yan ta'adda masu kashe kiristoci, cewar rahoton Daily Trust.
An ga jirage na shawagi a jihar Borno
Wani mazaunin yankin, Abba Dankale, ya ce hare-haren sama da Amurka ta kai a Jihar Sokkwato a Arewa maso Yammacin Najeriya, sun tsoratar da su matuƙa.
Dankale ya ce:
“Bayan sallar Asuba, mutane sun ga jiragen sama na shawagi, hakan ya sa muka ji tsoro sosai. Wasu daga cikin manoma da masunta ne kawai suka samu ƙarfin guiwa suka je gonakinsu da wuraren kamun kifi.
“Sannan mun gargadi manoma da masunta da ke gudanar da sana’o’insu a yankunan Dawashi, Dabar Giwa, Malam Karanti, Garin Malam Shuaibu, Daban Masara, Dunbulwa, Daban Gajere, da sauran wurare da su yi taka-tsantsan.
"Mu na ganin wadannan yankuna na iya zama wuraren da za a iya kawo hari sakamakon yawan jama’a da kuma ayyukan ’yan Boko Haram da ISWAP.”

Source: Getty Images
Mutane sun fara neman mafaka a Borno
Wani mazaunin ƙauye da bai bayyana sunansa ba ya bayyana cewa wasu manoma a Dawashi, Malam Karanti da wasu kauyuka sun fara ƙaura zuwa garin Baga.
A rahoton Chronicle, magidancin ya ce:
“Kun sani cewa a duk waɗannan yankuna babu isasshen tsaro. Mutanenmu suna zuwa wuraren ne domin noma da kamun kifi, amma galibi da yardar ’yan Boko Haram.
"Idan baku manta ba akwai lokacin da aka kashe manoman wake 40 a Dumba saboda ’yan ta’addan suka zarge su da bai wa sojoji bayanan sirri. Yankin ya sha fama da hare-hare da suka yi sanadiyyar mutuwar masunta sama da 23 a Tafkin Chadi.
“Hakan na cikin abubuwan da suka sa ake kallon waɗannan yankuna na da hadari. Ni ma na shawarci wasu daga cikin ’yan uwana da ke noma a wuraren da su dakata har sai al’amura sun lafa.
Sanata Ndume ya goyi bayan harin Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya roki gwamnatin Bola Tinubu da ta Amurka dasu fadada hadin gwiwar tsaro zuwa wasu yankuna na kasar.
Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, ya ce barazanar ‘yan ta’adda na ci gaba da damun yankin Arewa maso Gabas, musamman daga ISWAP da Boko Haram.
Ndume ya ce idan aka fadada irin wannan hadin gwiwa zuwa Arewa maso Gabas, za a raunana ISWAP da Boko Haram sosai.
Asali: Legit.ng

