Sojojin Najeriya Sun Ragargaza Boko Haram bayan Ndume Ya Nemi Daukin Amurka
- Dakarun Najeriya sun kai jerin hare-haren sama a Bama da suka yi sanadin kawar da manyan kwamandojin Boko Haram tare da raunana tasirinsu a yankin
- Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an yi hare-haren ne bisa aiki da sahihin bayanan sirri, lamarin da ya taimaka wajen samun nasarar aikin
- An samu wannan nasara ne kwanaki bayan Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya bayyana bukatar Amurka ta kawo hari kan mayakan Boko Haram a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Dakarun rundunar 'Operation Hadin Kai,' tare da goyon bayan sojojin kasa na Najeriya da kuma jiragen saman rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF), sun farmaki 'yan ta'adda a Borno.
Sojojin sun samu gagarumar nasara bayan da suka kai hare-haren sama a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, inda aka yi nasara a kan mayakan Boko Haram.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara bayan gwabza fada da 'yan bindiga a jihar Kano

Source: Facebook
Zagazaola Makama ya wallafa a shafin X cewa majiyoyin tsaro sun bayyana, hare-haren sun yi sanadin kawar da wasu manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram da ake dade ana nema a yankin.
Sojoji sun kawar da 'yan Boko Haram
Majiyoyin sun shaida cewa an kaddamar da hare-haren ne a ranar 25 ga Disamba, 2025, bayan samun sahihin bayanan sirri daga mutane a yankin da suka nuna motsin ‘yan ta’adda.
Wannan hadin gwiwa tsakanin bayanan sirri da karfin soji ya ba da damar kai farmaki a kan muhimman wuraren da ‘yan Boko Haram ke taruwa.
A cewar majiyoyin, akalla ‘yan ta’adda 10 ne suka mutu, daga cikinsu akwai Abul Kaka, Ibn Mu’azu, Abu Muhammad, Ba Alhaji, Bakura, Modu, Abu Hassan, Kaka Alai, Abba Yakariye da Bamusa.
Wadannan mutane na daga cikin jiga-jigan Boko Haram da suka dade suna taka rawa wajen shirya hare-hare a yankin Bama da kewaye.
Dakarun Sojoji sun raunata Boko Haram
Majiyoyin tsaro sun kara da cewa wani dan ta’adda mai suna Ubaida ya samu munanan raunuka a yayin harin, lamarin da ya rage masa karfin ci gaba da fafutuka.
Bayan harin farko, rundunar sojin sama ta Najeriya ta kai wani karin farmaki, wanda nan take ya hallaka wasu ‘yan ta’adda uku.

Source: Original
Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan wadanda aka kawar suna biyayya ne ga Bafu, wani shahararren kwamandan Boko Haram da ke aiki a yankin Bama.
Ndume ya nemi daukin Amurka a Borno
A wani labarin, mun wallafa cewa Ali Ndume ya yi magana kan hare-haren Amurka ta kai a jihohin Sokoto da Kwara, inda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta fadada hadin gwiwar zuwa yankin Arewa maso Gabas.
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya bayyana hakan ne yayin da yake yabawa hare-haren sama da aka kai kan sansanonin kungiyar ISIS a Tangaza, karamar hukumar Tambuwal a Sakkwato.
Ndume, wanda shi ne tsohon bulaliyar majalisa ya ce barazanar ‘yan ta’adda na ci gaba da addabar yankin Arewa maso Gabas, musamman daga ISWAP da Boko Haram, saboda haka ana bukatar agaji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
