Gwamna Abba na Shirin Barin NNPP, Wike Ya Aika Sakon Gargadi ga Masu Shiga APC

Gwamna Abba na Shirin Barin NNPP, Wike Ya Aika Sakon Gargadi ga Masu Shiga APC

  • Nyesom Wike ya bayyana cewa shiga jam'iyyar APC ko nuna biyayya ga Shugaba Bola Tinubu ba zai ba 'yan siyasa tikitin tazarce kai tsaye ba
  • Ya jaddada cewa dole ne a auna dan siyasa a kan alkawuran da ya cika da ayyukan da ya aiwatar, domin tantance wanda zai yi takara a 2027
  • Wike ya fara rangadin kananan hukumomin jihar Rivers domin karfafa siyasarsa yayin da ake shirye-shiryen zabuka a watanni masu zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya gargaɗi ‘yan siyasa cewa shiga APC ko nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu ba ya nufin tabbacin samun tikitin wa’adi na biyu kai tsaye.

Wike ya yi wannan gargaɗin ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a ƙaramar hukumar Emohua da ke jihar Rivers, a wani bangare na ziyarce-ziyarcensa na tuntubar jama'a a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Ana maganar makomar Kwankwaso da Ganduje yayin da Abba zai koma APC

Nyesom Wike ya gargdi masu shirin shiga APC da masu nuna goyon baya ga Tinubu
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike. Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Wike ya aika sako ga masu shirin shiga APC

Ministan, ya samu tarbar shugaban karamar hukumar Emohua, Chidi Lloyd, tare da sarkin gargajiya Sergeant Awuse da sauran shugabannin jam’iyya, in ji rahoton Channels TV.

A cewarsa, dole ne ƙabilar Ikwerre ta ci gaba da kasancewa mai tasiri a siyasar Najeriya, yana gargaɗi kan sakaci ko barazanar ware su daga tsarin siyasar kasar.

Wike ya bayyana cewa muhimmancin siyasa ana samun sa ne ta hanyar tsare-tsare da daidaito, ba wai a zo a canja tsari bayan an riga an yi nasara ba.

Wike ya ja kunnen masu goyon bayan Tinubu

Tsohon gwamnan Rivers ya ja kunnen 'yan siyasa cewa bayyana goyon baya ga Shugaba Tinubu, musamman bayan zaɓen 2023, ba zai ba su tabbacin samun tikitin tazarce ba.

Ya ƙara da cewa siyasa dole ta kasance bisa yarjejeniya, tare da cika alƙawura, yana mai cewa biyayya ba tare da tsari ko cika alƙawari ba, ba ta da wani alfanu ga jama'a.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da Shugaba Tinubu ya fi shi samu a fagen siyasar Najeriya

Tun da farko, shugaban ƙaramar hukumar Emohua ya tabbatar da cikakken goyon bayan yankin ga Shugaba Tinubu da Wike, yana mai cewa suna kan tafarkin siyasar da suka zaɓa.

Wike ya ce nuan goyon baya ga Tinubu ba shi zai ba dan siyasa damar samun tikitin tazarce ba.
Ministan Abuja, Nyesom Wike da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @GovWike, @DOlusegun
Source: Twitter

Tinubu, Wike sun samu goyon baya a Rivers

Daga Emohua, Wike ya wuce Isiokpo a ƙaramar hukumar Ikwerre, inda ya maimaita irin wannan saƙo, kamar yadda rahoton Premium Times.

A can, Samuel Nwanosike, shugaban hukumar kula da tsafta ta jihar Rivers, ya tabbatar da goyon bayan yankin ga Wike, yana musanta yiwuwar jam’iyyar ADC ta samu karɓuwa a yankin.

Masu lura da al’amura na ganin ziyarce-ziyarcen Wike a ƙasar Ikwerre na nuna ƙoƙarinsa na ƙarfafa tushen siyasar sa, yayin da kalamansa ke nuna yiwuwar sauye-sauyen siyasa kafin zaɓe mai zuwa a jihar Rivers.

Gwamna Abba na shirin shiga APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ana ta tattaunawa a fagen siyasar Kano kan yiwuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya ce yana da sahihin bayani cewa gwamnan zai koma APC nan da ‘yan makonni masu zuwa.

Bayanin ya haifar da martani iri-iri daga jama’a, inda wasu ke nuna shakku kan dalilan komawar, wasu kuma na ganin hakan cin amana ne ga masu kada kuri’a a jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com