Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah, Sun Sace Wasu Mutane a Gombe
- 'Yan bindiga sun kashe Yusuf da Faiza Mohammed a gidansu da ke Pindiga, sannan suka sace mutane hudu ciki har da kananan yara
- Rundunar 'yan sandan Gombe ta gano harsashai tare da tura dakaru na musamman domin bin sawun maharan da suka tsere daji
- Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana harin a matsayin "aikin dabbanci", inda ya lashi takobin cewa gwamnatin jihar za ta kamo 'yan bindigar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Wasu mahara da ba a tantance ko su wanene ba sun kutsa kai cikin wani gida a ƙauyen Pindiga da ke ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe, inda suka tafka ta'asa.
An rahoto cewa 'yan bindigar sun kashe wasu 'yan gida daya su biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane huɗu a safiyar ranar Lahadi, 28 ga Disamba, 2025.

Source: Original
'Yan bindiga sun kashe mutane 2 a Gombe
Waɗanda suka rasun su ne Yusuf Mohammed (ɗan shekara 31) da Faiza Mohammed (28), waɗanda aka harbe a gidansu da ke kan hanyar Pindiga zuwa Kashere da misalin ƙarfe 3:30 na dare, in ji rahoton Daily Trust.
Maharan sun kuma yi awon gaba da ƙanwarsu mai shekaru 16, Zainab Mohammed Yusuf.
Bayan wannan harin, 'yan bindigar sun zarce zuwa gidan Alhaji Yayaji Abdullahi a dai wannan ƙauyen, inda suka yi garkuwa da matarsa, Jummai Alhaji Yayaji (35), da yaransa biyu — Al’amin (11) da Fatima (14).
Wannan lamari ya jefa al'ummar yankin cikin babban tsoro da fargaba, musamman ganin yadda maharan suka yi ta harbi ba kakkautawa a cikin dare ba tare da tsoron jami'an tsaro ba.
Matakan da 'yan sanda suka dauka
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa jami'ai sun gano kwasfan harsashin AK-47 guda shida a wurin da abin ya faru.
Ya bayyana cewa rundunar ta tura jami'an binciken sirri da mafarauta da dakarun sa-kai domin bin sawun maharan tare da ceto waɗanda aka sace.
Likitoci a asibitin Cottage da ke Pindiga sun tabbatar da mutuwar Yusuf da Faiza jim kaɗan bayan an garzaya da su asibitin, in ji rahoton Punch.

Source: UGC
Gwamna Inuwa ya yi kakkausan martani
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya la'anci wannan hari, inda ya bayyana shi a matsayin aikin dabbanci da rashin imani wanda ba za a amince da shi ba.
Gwamnan, ta bakin kakakin sa Ismaila Uba Misilli, ya bayyana cewa kisan mazauna gari da sace mata da yara babban laifi ne ga bil'adama.
Ya bayar da umarnin tura duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin kamo maharan, yana mai gargaɗin cewa jihar Gombe ba za ta taɓa zama matasai ko mafaka ga masu aikata manyan laifuka ba.
Mutane 7 sun mutu a hanyar Gombe
A wani labari, mun ruwaito cewa, hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai, mazauna ƙauyen Lawanti da ke ƙaramar hukumar Akko a Gombe.
Hatsarin ya faru ne a kan babban titin Damaturu zuwa Maiduguri yayin da mutanen ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Maiduguri na jihar Borno domin halartar taron biki.
Wannan lamari ya jefa daukacin al'ummar Lawanti cikin wani hali na jimami da firgici sakamakon rasa rayukan matasa da kananan yara a lokaci guda.
Asali: Legit.ng


