‘Ba Mu Bukatar Taimakon Azzalumai’: Gumi Ya Soki Amurka kan Hari a Sokoto
- Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr. Ahmad Gumi ya magantu game da harin Amurka a wasu jihohin kasar guda biyu
- Gumi ya ce Najeriya na bukatar taimakon kasashen waje kan tsaro, amma ba daga masu laifuffuka, wariya ko masu tayar da zaune tsaye ba
- Malamin ya fadi haka ne a kafar sadarwa inda ya nuna damuwa kan irin kasashen ko kungiyoyin da ake neman taimakon tsaro daga gare su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Malamin addinin Musulunci, Dr. Ahmad Gumi, ya nuna damuwa game da hadin gwiwar Najeriya da Amurka.
Gumi ya ce Najeriya na bukatar taimakon kasa da kasa wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar.

Source: UGC
Gumi ya bayyana ra’ayinsa ne ta wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi 28 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan
'Fararen hula na cikin hatsari,' Jigon APC ya fadi kuskuren harin Amurka a Sokoto
Dalilin harin Amurka a jihohin Sokoto, Kwara
Kasar Amurka ta ce ta kai hare-hare kan yan ta'adda da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ne bisa bukatar gwamnati.
Harin ya auku a Arewa maso Yammacin kasar, a yankin jihar Sokoto inda jama'a suka ji ƙarar da ta girgiza wasu gidaje.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kai harin ne bayan gargaɗin cewa hakan za ta faru idan ba a daina kashe kiristoci ba.
Yadda gwamnatin Najeriya ta taimakawa Amurka
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da hare-haren Amrurka a Sokoto.
Ambasada Tuggar ya ce Najeriya ce ta bayar da bayanan sirri ga Amurka, kuma an yi aikin ne tare, ba tare da take yancin ƙasar ba.
Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa hare-haren ba su da alaƙa da addini, illa yaki da ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyi.

Source: Facebook
Martanin Gumi kan taimakon Amurka a Najeriya
Sai dai ya jaddada cewa bai kamata a karbi irin wannan taimako daga kasashe ko kungiyoyin da ya bayyana a matsayin masu aikata laifi ba.
Gumi ya kalubalanci tushen taimakon tsaron da ake nema musamman duba da yadda Amurka ta shiga lamarin.
A cewarsa, babu shakka kowace kasa na bukatar taimakon waje a wani lokaci domin kare tsaronta da rayukan al’ummarta.
Ya ce:
“Lamarin yana da sauƙi, Shin muna buƙatar taimako? Eh, kowace ƙasa na buƙatar taimako wajen tsaronta.
"Amma ba daga masu aikata laifi da ba sa girmama dokokin ƙasa da ƙasa, masu wariya, masu tsattsauran ra’ayin addini, da waɗanda aka sani suna taimaka wa kisan kare dangi a duniya ba.”
Amma Sheikh Gumi ya gargadi cewa dogaro da masu wariya, tsattsauran ra’ayi ko masu kisan kare dangi na iya kara tabarbarewar matsalar tsaro maimakon warwareta.
Gumi ya soki harin Amurka a Sokoto
Mun ba ku labarin cewa fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da duk wani haɗin gwiwar soji da Amurka nan take.
Malamin ya yi gargaɗin cewa tsoma bakin Amurka na iya maida Najeriya filin yaƙi musamman bayan harin da ta kai wani kauye da ke jihar Sokoto.
Sheikh Gumi ya ba da shawarar a nemi taimakon soji daga ƙasashe masu “tsaka-tsaki” kamar China, Turkiyya da Pakistan domin magance matsalolin ƙasar.
Asali: Legit.ng

