'Fararen Hula na cikin Hatsari,' Jigon APC Ya Fadi Kuskuren Harin Amurka a Sokoto

'Fararen Hula na cikin Hatsari,' Jigon APC Ya Fadi Kuskuren Harin Amurka a Sokoto

  • Adamu Garba ya soki Amurka kan harba makami mai linzami a Najeriya, wanda ya ce an yi ba tare da hadin gwiwar sojojojin kasar ba
  • Ya bayyana cewa rashin sa hannun sojoji wajen jagorantar harin na ranar Kirsimeti babbar barazana ce ga martabar Najeriya
  • Adamu ya yi gargadin cewa irin wannan harin na bai-daya na iya jefa rayuwar farar hula cikin hadari kamar yadda ya faru a Somalia

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC, Adamu Garba, ya bayyana damuwarsa game da harin sama da ƙasar Amurka ta kai a cikin Najeriya.

Adamu Garba ya bayyana cewa wannan mataki ya raina martaba da kuma ƙwarewar dakarun sojin Najeriya, waɗanda ya kamata a ce sune a gaba wajen jagorantar kowane irin samame na yaƙi da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Malam Nata'ala da wasu fitattun jaruman Kannywood da suka rasu a 2025

Adamu Garba ya gargadi gwamnatin Najeriya game da kyale Amurka ta kawo hari kasar
Shugaban Amurka, Donald Trump da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @realDonaldTrump, @officialABAT
Source: UGC

Adamu Garba ya ga laifin harin Amurka

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, Adamu Garba ya ce ko da yake yana goyon bayan haɗin gwiwa da Amurka, harin da aka kai a ranar Kirsimeti ya saɓa wa dukkan tsammani.

Ya soki yadda Amurka ta harba makami mai linzami na "Tomahawk" ba tare da an ga jami'an sojin Najeriya a wurin ba don daidaita yadda harin zai kasance.

A cewar tsohon dan takarar shugaban kasar, yin hakan ya rage darajar sojojin Najeriya zuwa matsayin masu kwashe tarkace kawai.

Barazanar tsaro ga farar hula a Najeriya

Adamu Garba, wanda kuma shi ne Babban Daraktan Cibiyar Ci Gaban Afirka (CAPD), ya nuna damuwa kan yadda tarkacen makamin ya shafe sa'o'i 48 a wurin harin ba tare da jami'an tsaron Najeriya sun kwashe su ba.

Ya yi gargaɗin cewa idan aka bar Amurka tana jagorantar irin waɗannan hare-hare ba tare da sanya sojin Najeriya a gaba ba, babu ɗan Najeriyar da zai tsira a cikin gidansa.

Kara karanta wannan

Dalilin Donald Trump na jinkirta kai hari a Najeriya zuwa ranar Kirsimeti

A cewarsa, sai bango ya tsage ne kadangare ke samun kofar shiga, wanda ke nufin Amurka na iyakai hari kowane lokaci ta ga dama sunan yaƙi da 'yan ta'adda a Najeriya.

Adamu Garba ya gargadi gwamnatin Najeriya bayan harin Amurka a Sokoto
Adamu Garba, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC. Hoto: @adamugarba
Source: Twitter

Misalin halin da wasu kasashe suka shiga

Dan siyasar ya bayar da misali da abin da ya faru a ƙasashen Somalia, Yemen, Pakistan, da Libya, inda ya ce hare-haren Amurka na tsawon shekaru 30 a Somalia bai kawo ƙarshen ta'addanci ba, face ma ƙara rura wutar fitina.

Adamu Garba ya jaddada cewa rashin tsari da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu na iya sa al'amura su ƙara tabarɓarewa maimakon a samu zaman lafiya.

Ya buƙaci gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ta fito fili ta yi bayani kan wannan haɗin gwiwa domin kwantar wa jama'ar Najeriya hankali.

Ndume ya magantu kan harin Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Ali Ndume ya roki gwamnatin Bola Tinubu da ta Amurka da su fadada hadin gwiwar tsaro zuwa wasu yankuna na kasar.

'Dan majalisar ya bukaci gwamnatocin biyu da su fadada har zuwa Arewa maso Gabas saboda barazanar 'yan ISWAP da Boko Haram.

Sanata Ndume ya yaba wa hare-haren sama da aka kai kan sansanonin ISIS a Sokoto, yana mai cewa irin wannan aiki zai raunana ‘yan ta’adda matuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com