Ana Wata ga Wata: An Maka Wike da Gwamnoni 36 a Kotu kan Naira Tiriliyan 14

Ana Wata ga Wata: An Maka Wike da Gwamnoni 36 a Kotu kan Naira Tiriliyan 14

  • Kungiyar SERAP ta shigar da kara a gaban kotu tana neman a tilasta wa gwamnoni da ministan Abuja bayyana yadda suka kashe N14trn
  • Karar ta nuna damuwa kan yadda kudaden rarar tallafin mai ba su rage radadin talauci ko inganta fannin ilimi da lafiya a jihohi ba
  • SERAP ta jaddada cewa hakkin 'yan Najeriya ne su san yadda ake amfani da dukiyar gwamnati domin tabbatar da gaskiya da rikon amana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kare hakkin jama'a da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta shigar da kara gaban babban kotun tarayya da ke Legas tana kalubalantar gwamnonin jihohi 35 da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

SERAP tana zargin wadannan shugabanni da gazawa wajen bayyana yadda aka kashe kimanin Naira tiriliyan 14 da aka samu a matsayin rarar kudaden da aka tara bayan janye tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

SERAP ta yi karar gwamnoni da ministan Abuja
Kungiyar gwamnonin Najeriya suna yin taro a Abuja. Hoto: @NGFSecretariat
Source: Facebook

SERAP ta maka Wike da gwamnoni a kotu

Ta ce an kashe kudaden ne tun daga watan Mayun 2023 yayin da ta hada da ofishin Akanta-Janar na tarayya a cikin wadanda ake kara, in ji rahoton Punch.

A cikin sanarwar da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, kungiyar ta bayyana cewa duk da karuwar kudaden da jihohi ke samu daga asusun tarayya (FAAC), hakan bai sauya rayuwar talakawa ba.

SERAP ta bukaci kotu da ta tilasta wa gwamnonin da minista Wike su fito su bayyana daki-daki wuraren da aka aiwatar da ayyuka da wadannan kudade, tare da nuna irin tasirin da hakan ya yi kan fannin lafiya da ilimi ga marasa karfi.

Kalubalen rashin gaskiya da hakkin talakawa

Lauyoyin kungiyar, Oluwakemi Agunbiade da Valentina Adegoke, sun bayyana cewa kudaden da aka raba wa jihohi sun karu da kashi 45.5, inda a halin yanzu rabon kowane wata ke wuce Naira tiriliyan 1.6.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi jiha 1 da za ta iya tatso Naira tiriliyan 1 daga gidaje duk shekara

SERAP ta nuna damuwa cewa duk da wannan dumbin dukiya, da yawa daga cikin jihohi har yanzu suna karbo bashi domin biyan albashi da fansho, kamar yadda aka wallafa a shafin kungiyar.

Yayin da ake karbo bashin kudi, SERAP ta ce miliyoyin ‘yan Najeriya na rayuwa cikin matsanancin hali ba tare da samun ababen more rayuwa na yau da kullum ba.

SERAP tana so a tilasta Wike da gwamnoni su bayyana yadda suka kashe kudaden
Nyesom Wike, ministan Abuja da SERAP ta maka a kotu. Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Hujjojin SERAP na shigar da kara

Kungiyar ta kafa hujja da sassan 13, 15(5), da 16(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa ta Majalisar Dinkin Duniya.

SERAP ta jaddada cewa talakawa ne suka fi shan wahalar janye tallafin man fetur, saboda haka ya kamata kudaden su koma wajen rage musu radadi.

Har yanzu kotu ba ta tsayar da ranar da za ta fara sauraron wannan kara mai lamba FHC/L/MSC/1424/2025 ba, wadda aka shigar ranar Juma'ar da ta gabata.

SERAP ta yi karar bankin CBN

A wani labarin, mun ruwaito cewa, SERAP ta maka babban bankin Najeriya (CBN) ƙara a bisa zargin gaza yin bayanin inda sama da N100bn na yagaggun kuɗi suka yi.

Kara karanta wannan

'An kusa gama gyara lantarkin Najeriya,' Ministan makamashi ya yi albishir

SERAP ta ce tana kuma ɗaukar matakin shari’a a kan CBN saboda N12bn da aka warewa ofisoshin babban bankin a Abeokuta, jihar Ogun, da kuma Dutse a jihar Jigawa.

Wani dalili kuma da ya sa ƙungiyar SERAP ta kai ƙarar babban bankin Najeriya a gaban kotu shi ne bashin Naira biliyan uku da aka ba jihohin Anambra da Enugu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com