Abin da Muka Sani game da Jita Jitar Harin Amurka Ya Hallaka Turji a Sokoto
- Da safiyar yau Lahadi 28 ga watan Disambar 2025 aka fara yada rade-radin harin Amurka da aka kai a Sokoto ya yi ajalin Bello Turji
- Amurka dai ta kai harin ne a ranar Kirsimeti kan wasu yan ta'adda da ta kira da yan kungiyar ISIS a wasu yankuna
- Masu bincike sun ce labarin kisan Turji ya samo asali ne daga bayanan bogi da suka dade da aka sake yadawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Akwai rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu shafukan labarai cewa an kashe fitaccen shedanin dan bindiga, Bello Turji.
An ce Bello Turji ya mutu ne a wani harin sama da kasar Amurka ta kai, sai dai an tabbatar da cewa ba su da tushe.

Source: Facebook
Rade-radin da ake yadawa kan Bello Turji
Sai dai shafin Zagazola Makama ya tabbatar da cewa Bello Turji yana raye, kuma a halin yanzu yana boye a yankin Dubagale.
Yankin Dubagale na Arewacin kauyen Dan Adama, a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
Binciken ya nuna cewa wurin da Bello Turji ke fakewa na kusan kilomita 25 ne daga iyakar Jamhuriyar Nijar, lamarin da ke nuna yadda yake ci gaba da tserewa zuwa yankunan da ke kusa da kan iyaka.
Masu binciken sun jaddada cewa ba a kashe Bello Turji a kowane irin harin sama ba, inda suka ce labaran da ke ikirarin hakan ƙirƙirarre ne.

Source: Original
Babu gaskiya kan jita-jitar mutuwar Bello Turji
Rahoton ya kara da cewa wadannan jita-jitan sun samu karbuwa ne sakamakon bayanan bogi da tsofaffin labarai da ake sake yadawa musamman a lokacin da aka tsaurara ayyukan yaki da ‘yan bindiga a wasu sassan Najeriya.
Bello Turji, wanda hukumomi ke nema ruwa a jallo tsawon lokaci, na gudanar da ayyukansa ne musamman a jihar Zamfara da wasu jihohin makwabta.
An danganta shi da hare-haren kisa, satar mutane da dama, da kuma tilasta wa al’ummomi barin muhallansu a yankin.
Shafin Bakatsine ma ya ba da rahoto game da jita-jitar hallaka Turji wanda ya wallafa a shafin X.
Sai dai rahoton ya ce babu tabbaci kan labarin da ake yadawa yayin da ake ci gaba da bincike don gano gaskiyar lamarin.
Wannan ba shi ne karon farko ba da ake yada mutuwar Bello Turji wanda daga bisani yake tabbata karya ne.
Masanin tsaro ya magantu game da Turji
A baya, mun ba ku labarin cewa wani masanin tsaro a Najeriya, Yahuza Getso ya bayyana cewa Bello Turji bai buya a ko ina ba kamar yadda ake zaton cewa yana gudun neman tsira.
Dr Getso ya bayyana cewa matukar gwamnati da gaske ta ke, tsaf za ta tabbatar da cewa dakarun Najeriya sun yi ram da shi a kasa da awanni 24.
Bayaninsa na zuwa ne a lokacin da Najeriya ta dauki zafi game da zarge-zargen da ake yi wa Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle na ta'addanci.
Asali: Legit.ng

