Harin Amurka Ya Tarwatsa ’Yan Ta’adda, Suna Tserewa Zuwa Wasu Yankunan Arewa

Harin Amurka Ya Tarwatsa ’Yan Ta’adda, Suna Tserewa Zuwa Wasu Yankunan Arewa

  • Ana zargin ‘yan ta’adda a Arewa na fara guduwa daga maboyarsu bayan hare-haren sama da Amurka ta kai a Sokoto
  • Sarakunan gargajiya da jami’an tsaro sun ce hare-haren sun tarwatsa sansanonin ‘yan bindiga zuwa wasu yankuna
  • Masana tsaro sun gargadi cewa ‘yan ta’addan na iya cakuduwa da fararen hula ko kuma neman tallafi daga kungiyoyin ta’addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Akwai alamun cewa ‘yan ta’adda sun fara sauya matsuguni bayan hare-haren makamai masu linzami da kasar Amurka ta kai.

Wannan bulaguro na da nasaba da harin Amurka a jihohin Sokoto da Kwara da aka ce an yi domin yan ta'adda.

An gano wasu yan ta'adda na sauya matsuguni bayan harin Amurka
Shuagaba Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Shugabannin al’umma sun shaida wa Punch cewa sun lura da shige da ficen ‘yan bindigar bayan hare-haren da aka kai a ranar Kirsimeti.

Harin da Amurka ta kai Sokoto, Kwara

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya hango yiwuwar kuskure game da harin Amurka a Najeriya

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar cewa sojojin Amurka sun kai hare-hare masu muni kan ‘yan ta’addan ISIS a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da harin, tana mai cewa ta bayar da cikakken goyon baya, kuma an kai hare-haren ne a wuraren da ‘yan ta’addan ke amfani da su.

A Jabo, karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto, makami ya fado ne a gonaki, yayin da wasu gine-gine suka lalace a Offa, jihar Kwara.

Jami’an karamar hukumar Tangaza a Sokoto sun ce an kuma kai wasu hare-hare kan maboyar kungiyar ‘yan bindiga ta Lakurawa a wasu sassan yankin Sokoto.

Yawaitar ‘yan bindiga a Benue

Shugaban majalisar gargajiya ta Gwer ta Yamma a jihar Benue, Daniel Abomtse, ya ja hankalin jama’a kan shigowar makiyaya masu dauke da makamai zuwa wasu al’ummomi.

Da yake magana, basaraken ya ce ya lura da zuwan makiyaya dauke da manyan makamai a yankinsa da kuma karamar hukumar Agatu.

Ya ce suna tserewa ne daga Sokoto zuwa yankunan Benue, suna kiwo a fili tare da manyan makamai.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ndume ya roƙi Tinubu da Donald Trump game da yaƙi da ta'addanci

Ya ce wannan hari shi ne abu mafi kyau da ya faru ga Najeriya tun bayan bullar matsalar tsaro shekaru 16 da suka gabata, cewar Daily Post.

Yan ta'adda na tserewa zuwa Benue daga Sokoto
Taswirar jihar Benue da ke Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Amurka ta koma sa ido a Sambisa

Wani dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya ce hare-haren sun hana yiwuwar kai farmaki a lokacin Kirsimeti, yana mai cewa Kiristoci da dama sun rasa rayukansu a bukukuwan baya.

Har ila yau, an gano cewa Amurka ta koma sa ido ta sama (ISR) a dajin Sambisa da ke jihar Borno, inda wani jirgin Gulfstream V ke shawagi domin tattara bayanan sirri kan ISWAP.

An bukaci Trump ya kai hari Benue

An ji cewa shugaban Mzough U Tiv ya yaba wa Donald Trump kan fara hare-hare, yana mai cewa Benue ma na bukatar hakan.

Sarkin ya ce tsawon shekaru ana kashe manoma da lalata kauyuka a Benue, lamarin da ya tilasta dubban mutane barin muhallansu.

Ya nemi a ci gaba da hare-haren tare da faɗaɗa su zuwa Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.