Daga Tafiya Daurin Aure, Mutane 7 'Yan Gari Daya Sun Mutu a Jihar Gombe

Daga Tafiya Daurin Aure, Mutane 7 'Yan Gari Daya Sun Mutu a Jihar Gombe

  • Mutane bakwai a jihar Gombe sun riga mu gidan gaskiya a wani mummunan hatsarin mota kan hanyar Maiduguri ranar Asabar
  • An ce mutanen sun rasu ne a hanyar zuwa daurin aure daga Gombe zuwa Maiduguri, lamarin da ya jefa mutane a tashin hankali
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar matasan a matsayin babban rashi mai radadi ga iyalansu da kuma al'ummar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a ranar Asabar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai, dukkaninsu mazauna ƙauyen Lawanti da ke ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe.

Hatsarin ya faru ne a kan babban titin Damaturu zuwa Maiduguri yayin da mutanen ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Maiduguri na jihar Borno domin halartar taron biki.

Kara karanta wannan

Hankula sun girgiza bayan bama bamai sun tashi da matafiya a Zamfara

'Yan gari daya har su bakwai sun mutu a hanyar zuwa daurin aure a Gombe.
Taswirar jihar Gombe, inda mutane 7 'yan gari daya suka mutu a hanyar zuwa daurin aure. Hoto: Legit.g
Source: Original

Sunayen mutanen da suka mutu a Gombe

Wannan lamari ya jefa daukacin al'ummar Lawanti cikin wani hali na jimami da firgici sakamakon rasa rayukan matasa da kananan yara a lokaci guda, in ji rahoton Daily Trust.

Wadanda suka riga mu gidan gaskiya sun hada da Gambo Abbo (dan shekara 35), Umalkhairi (18), Rabiu Abubakar (28), Fatuma Hassan (28), Amal Abubakar (3), Adamu Bello (4), da kuma Zara’u Alhaji (27).

Rundunar ceto ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon lalacewar titi ko gudun wuce kima, kodayake ana ci gaba da binciken musabbabin faruwar lamarin.

Rasa wadannan rayuka ya bar babban gibi ga iyalansu, musamman ganin yadda wasu daga cikinsu ke da kyakkyawan fata na samun nasara a rayuwa.

Gwamna Yahaya ya mika sakon ta'aziyya

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana wannan hatsari a matsayin babban rashi mai raɗaɗi ga jihar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnoni 19 suka ce kan bam din da ya tashi a masallacin Juma'a a Maiduguri

A cikin wata sanarwa da kakakin sa, Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya ce babu kalmomin da za su iya kwantar da hankalin iyalan da suka rasa masoyansu a irin wannan hali.

Gwamnan ya mika ta'aziyya ta musamman ga shugabannin al'ummar Lawanti da kuma kansila mai wakiltar yankin wadanda suka rasa 'yan uwa na kusa a hatsarin.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi alhinin rasuwar mutane 7 a hatsarin mota a Gombe.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya. Hoto: @GovernorInuwa
Source: Facebook

Iyalan wadanda suka rasu sun yi magana

Malam Idris Lawanti, wani uba da ya rasa 'ya'yansa mata guda biyu a hatsarin, ya bayyana wa manema labarai cewa daya daga cikinsu na gab da kammala karatun aikin jinya (nursing school), yayin da daya ke aji biyu na sakandare (SS2).

Ya bayyana cewa wannan rashi ya taba zuciyarsa kwarai da gaske, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamna Yahaya ya yi addu'ar Allah ya gafarta musu kurakuransu, ya sa Aljannar Firdausi ce makomarsu, sannan ya bai wa iyalan hakurin jure wannan rashi.

Gwamnatin jihar ta kuma bukaci direbobi da su rika kiyaye dokokin titi musamman a wannan kakar na tafiye-tafiyen biki.

Wata 'yar garin Akko, Hafsat Akko da ta zanta da Legit Hausa ta bayyana kaduwarta game da rasuwar wadannan mutane, tana mai cewa al'ummar garin sun shiga damuwa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fitar da bayanai kan harin bam a masallacin Maiduguri

"Mun shiga dimuwa sosai da muka ji labarin rasuwar su Amal. Mutanen da suka tafi biki an dawo da gawarsu gida, ka san wannan dole ya sosa zukatanmu.
"Amma wannan na daga cikin kaddarar rayuwarmu, dole za mu mutu wata rana kamar yadda aka haife mu. Allah ya jikansu da Rahama, ya sa mutu ta zama hutu a gare su."

- Hafsat Akko.

Jagoran SDP ya rasu a hadarin mota

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan siyasa a Kaduna sun shiga damuwa bayan rasuwar daya daga cikin jiga-jigai, kuma masu fada a ji a garin Zariya.

Wannan ya biyo bayan rasuwar Bashir Zakariya, shugaban jam’iyyar SDP na yankin Zariya, a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da shi.

Jam’iyyar SDP ta bayyana marigayin, Bashir Zakariya a matsayin mutum mai gaskiya da hangen nesa, wanda ya sadaukar da kansa ga adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com