Hadimin Tinubu Ya Hango Yiwuwar Kuskure game da Harin Amurka a Najeriya
- Hadimin shugaba Bola Tinubu Daniel Bwala ya yi magana game da harin da Amurka ta kawo a Najeriya
- Bwala ya bayyana hare-haren sama da Amurka ta kai wa ‘yan ta’adda a Sokoto a matsayin abin da ke cike da “ruɗani”
- Ya ce duk da ikon da Amurka ke da shi kan yaƙi da ISIS a duniya, babu tabbacin ta samu amincewar majalisarta kan haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Mai ba Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Daniel Bwala, ya magantu kan harin Amurka.
Bwala bayyana hare-haren sama da kasar Amurka ta kai kan ‘yan ta’adda masu alaka da ISIS a jihar Sokoto a matsayin abin da ke cike da shakku.

Source: Twitter
Hadimin Tinubu ya magantu kan harin Amurka
Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da gidan talabijin na Sky News.
Ya ce duk da cewa Amurka na da ikon gudanar da hare-hare kan kungiyar ISIS a duniya, amma babu tabbacin cewa Majalisar Dokokin Amurka ta ba ta izinin yakar kungiyoyin ta’adda da aka ayyana a Najeriya.
Ya ce:
“Na tabbata gwamnatin Amurka na da ikon shari’a na kai hare-hare kan ISIS da rassanta a ko’ina a duniya. Amma mai yiwuwa ba ta samu cikakken izini daga Majalisar Dokokinta na yakar kungiyoyin ta’adda da aka ayyana a Najeriya ba.”

Source: Twitter
Hare-haren da ISIS ke yi a Afirka
Kungiyar ISIS, wacce aka fi sani da Islamic State ko ISIL, kungiya ce mai tsattsauran ra’ayin addini wacce ke dauke da akidar jihadi, kuma ta kai hare-hare a kasashe da dama na duniya, ciki har da nahiyar Afirka.
Burinta shi ne kafa abin da take kira da daular Musulunci bisa tsattsauran fahimtar dokokin Musulunci.
Najeriya na fama da matsanancin rashin tsaro da ta’addanci tun shekarar 2009. A farkon shekarun rikicin, kungiyar Boko Haram ce ke daukar nauyin mafi yawan hare-haren.

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi albishir ga 'yan Najeriya game da karbo wasu jiragen yaki daga Amurka
Sai dai a ‘yan shekarun nan, wasu kungiyoyin ta’adda sun bayyana, ciki har da Ansaru, ISWAP, Lakurawa da sauransu, wadanda aka danganta da ISIS.
Wadannan kungiyoyi na kai hare-hare kan al’ummomin Najeriya, a watan Oktoba, wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa ana ci gaba da kisan kiyashi a Najeriya.
Daga bisani, Amurka ta sake ayyana Najeriya a matsayin kasa a jerin CPC, bayan Shugaba Donald Trump ya bayyana fargabar cewa Kiristanci na fuskantar barazana mai tsanani a kasar.
Dan majalisar Amurka ya magantu kan hari
An ji cewa 'dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi tsokaci kan harin da kasarsa ta kawo Najeriya kan 'yan ta'adda a ranar Kirsimeti.
Riley Moore ya bayyana cewa a wannan shekarar Amurka ta ba 'yan ta'adda masu tsatstsauran ra'ayi kyauta a lokacin Kirsimeti.
'Dan majalisar ya nuna cewa harin ya yi nasarar hana abin da ya kira kisan da ake yi wa Kiristoci a lokacin Kirsimeti a Najeriya.
Asali: Legit.ng
