Harin Amurka: Ndume Ya Roƙi Tinubu da Donald Trump game da Yaƙi da Ta'addanci
- Sanata Ali Ndume ya roki gwamnatin Bola Tinubu da ta Amurka da su fadada hadin gwiwar tsaro zuwa wasu yankuna na kasar
- 'Dan majalisar ya bukaci gwamnatocin biyu da su fadada har zuwa Arewa maso Gabas saboda barazanar 'yan ISWAP da Boko Haram
- Ndume ya yaba wa hare-haren sama da aka kai kan sansanonin ISIS a Sokoto, yana mai cewa irin wannan aiki zai raunana ‘yan ta’adda matuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Shugaban Masu Tsawatar wa a Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ya magantu game da harin Amurka a jihohin Sokoto da kuma Kwara.
Sanata Ndume ya bukaci gwamnatin tarayya ta fadada hadin gwiwar soji da Amurka zuwa Arewa maso Gabas.

Source: Twitter
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin yabawa hare-haren sama da aka kai kan sansanonin ISIS a Tangaza, karamar hukumar jihar Sokoto, cewar Punch.
Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, ya ce barazanar ‘yan ta’adda na ci gaba da damun yankin, musamman daga ISWAP da Boko Haram.
Harin Amurka a Sokoto da Kwara
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da hare-haren da aka kai inda ya ce an kai jerin hare-haren da aka tsara sosai.
Trump ya bayyana cewa ma’aikatar tsaron Amurka ce ta jagoranci hare-haren domin lalata karfin ‘yan ta’addan ISIS da ke yankin.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya tabbatar da cewa an gudanar da aikin da sahalewar Najeriya gaba daya.
Tuggar ya jaddada cewa hare-haren ba su karya ikon kasar Najeriya ba, kuma ba su da nasaba da nuna wariya ta addini.
Rokon Ndume ga Tinubu & Trump
Ndume ya ce idan aka fadada irin wannan hadin gwiwa zuwa Arewa maso Gabas, za a raunana ISWAP da Boko Haram sosai.
Tsohon 'dan majalisar wakilan ya bayyana cewa ‘yan ta’addan na da manyan maboyarsu uku: Tafkin Chadi, tsaunukan Mandara, da dajin Sambisa.

Source: Facebook
Bukatar Ndume kan yaki da ta'addanci
Ya kuma nemi a samar da jiragen yakin sama masu saukar ungulu domin tallafawa sojojin kasa a yayin fafatawa da ‘yan ta’adda.
Ndume ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ware mafi girman kasafin kudi ga tsaro a kudirin kasafin 2026, cewar TheCable.
Sai dai ya bukaci a tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma yadda za a kashe kudaden tsaron yadda ya dace.
Dangane da harin kunar bakin wake a masallacin Gamboru, Maiduguri, Ndume ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.
Harin ya kashe mutane biyar tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya sake nuna muguntar ‘yan ta’adda a yankin.
Trump ya magantu kan hari a Najeriya
An ji cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya magantu bayan kai harin sojojinsa kan wasu 'yan ta'adda a jihar Sokoto da ke Najeriya.
Trump ya ce ya sauya ranar kai harin soji kan ’yan ISIS a Najeriya zuwa ranar Kirsimeti domin wani dalili na musamman.
Masu lura da al’amura sun ce harin na iya kasancewa wata dabara don faranta ran Kiristocin masu ra’ayin mazan jiya.
Asali: Legit.ng

