Murnar Aure Ya Koma Bakin Ciki, Harsashen Bindiga Ya Kashe Matashi a Gombe

Murnar Aure Ya Koma Bakin Ciki, Harsashen Bindiga Ya Kashe Matashi a Gombe

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa wani matashi mai shekaru 19, ɗan ƙungiyar mafarauta, ya rasa ransa yayin bikin aure
  • An ce lamarin ya faru ne sakamakon fitar harsashe da ya faru bisa kuskure a wata unguwa da ke Arewacin birnin Gombe.
  • Rahoto ya ce lamarin ya faru ne yayin da yake halartar bikin auren abokinsa, inda bindigar da ya ke rike da ita ta carke, harsashen ya fita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Rahotanni sun tabbatar da cewa wani matashi ya rasa ransa yayin wani bikin auen abokinsu da ake yi a jihar Gombe.

Matashin mai shekaru 19 wanda ɗan ƙungiyar mafarauta ne, ya mutu sakamakon fashewar bindiga ba tare da gangan ba a unguwar Alkahira da ke Jihar Gombe.

Matashi ya mutu a bikin aure a Gombe
Kakakin rundunar yan sanda a Gombe, Buhari Abdulahi. Hoto: Buharee Abdullahi Dan Romi.
Source: Facebook

Matashi ya mutu a bikin aure a Gombe

Kara karanta wannan

An samu gawar ma'aikaci a gidan gwamnatin Gombe cikin halin ban mamaki

Rahoton Zagazola Makama ya bayyana cewa mamacin, mai suna Tanko Abubakar wanda aka fi sani da Walid, ya rasu yayin halartar bikin auren wani abokinsa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gudanar da auren a ranar 26 ga Disambar 2025 da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.

An ce Tanko yana rike da bindigar ne domin harbawa sama a yayin murnar bikin auren, kamar yadda aka saba a wasu al’adu.

Sai dai rahoton ya nuna cewa bindigar ta makale, kuma yayin da ya duba bakin bindigar cikin sakaci, sai ta fashe ba zato ba tsammani.

An tabbatar da mutuwar matashi bayan harbin harsashe bisa kuskure a Gombe
Taswirar jihar Gombe da ke tsakiyar Arewa maso Gabas. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka sanar da mutuwar matashin

Harsasan bindigar sun bugi kansa, lamarin da ya sa aka garzaya da matashin Asibitin kwararru na Gombe domin samun agajin gaggawa.

Sai dai likitoci sun tabbatar da mutuwarsa bayan isarsa asibitin, inda aka ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin.

Rahoton ya ƙara da cewa an sanar da iyalansa game da faruwar lamarin domin ɗaukar matakan da suka dace.

A halin yanzu, hukumomi sun shawarci jama’a da su guji wasa da makamai, tare da yin taka-tsantsan sosai wajen sarrafa bindiga ko kowanne irin makami.

Kara karanta wannan

An kama kasurgumin 'dan bindiga mai nuna miliyoyin kudi a intanet

Sun jaddada cewa irin wannan sakaci na iya janyo asarar rayuka, musamman a lokutan bukukuwa da taron jama’a.

Wani matashi ya yi magana da Legt Hausa

Wani dan unguwar, Khalid Muhammad ya ce lamarin ya tayar da hankulan mazauna yankin da kewaye.

Ya ce:

"A lokacin aka yi gaggawar daukarsa zuwa 'general' (Asibitin kwararru) amma a can aka tabbatar da mutuwarsa."

Khalid ya shawarci matasa da su yi hankali musamman wasanni da ake yi a lokatan bukukuwan aure da kuma wasa da babura saboda hatsarin da ke ciki.

An samu gawa a gidan gwamnatin Gombe

Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun ce an tsinci gawar wani ma’aikacin wucin-gadi da ke aiki a Gidan Gwamnatin Jihar Gombe.

Rahotanni sun ce an garzaya da shi zuwa asibiti bayan ganin shi kwance babu rai, sai dai daga bisani likitoci sun ce ya rasu.

Tuni yan sanda suka cafke wani mutum da ake zargi da hannu a kisan, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.