Jam'iyyar PDP Ta Soki Gwamna da Ya Yi Gum da Bakinsa bayan Harin Amurka

Jam'iyyar PDP Ta Soki Gwamna da Ya Yi Gum da Bakinsa bayan Harin Amurka

  • Jam’iyyar PDP mai adawa a Kwara ta caccaki gwamnatin jihar bayan harin Amurka a ranar Alhamis 25 ga watan Disambar 2025
  • PDP ta yi martanin ne kan shiru da gwamnatin jihar ta yi bayan fashewar bam a Offa, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba
  • Jam'iyyar ta ce tun bayan fashewar a daren Kirsimeti, babu jawabi, bayanin tsaro ko ziyarar jami’an gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Jam’iyyar PDP a Kwara ta soki gwamnatin jihar kan rashin mayar da martani bayan fashewar da ta auku a Offa.

Jam'iyyar PDP ta ce shiru da gwamnatin ta yi ya bar mazauna Offa cikin damuwa, tsoro da neman karin bayani kan abin da ya faru.

PDP ta caccaki gwamnan Kwara kan harin Amurka
Gwamna Abdul Rahman AbdulRazak na jihar Kwara da tambarin PDP. Hoto: Kwara State Government.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da shafin jam'iyyar PDP reshen jihar Kwara ya wallafa a manhajar Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

PDP ta jajantawa mutanen Offa a Kwara

A wata sanarwa daga Ilorin, PDP ta ce gwamnatin AbdulRahman AbdulRazaq ta kasa yi wa jama’a jawabi ko basu tabbacin tsaro tun faruwar lamarin.

Jam’iyyar ta jajanta wa mutanen Offa, ciki har da Olofa na Offa, Mufutau Gbadamosi Esuwoye I, da ’yan kasuwa da al’ummomin da abin ya shafa.

PDP ta ce abin takaici ne yadda jama’a ke tserewa cikin firgici, alhali gwamna da gwamnatinsa ba su fitar da ko sadarwa ba.

Ta kara da cewa babu wani bayani a hukumance, taron tsaro, ko ziyarar jami’an gwamnati domin kwantar da hankalin jama’ar jihar.

PDP ta bayyana cewa gibin shugabanci irin wannan na haddasa jita-jita, firgici da yaduwar tsoro a tsakanin ’yan kasa marasa laifi.

Harin Amurka a Kwara ya fusata PDP
Taswirar jihar Kwara da Amurka ta kai hari wani yanki. Hoto: Legit.
Source: Original

Jam’iyyar ta ce gwamnati mai alhaki za ta gaggauta ziyartar wurin, ta tantance halin da ake ciki, tare da sanar da jama’a gaskiya.

Martanin PDP kan harin Amurka a Kwara

PDP ta soki gwamnati da cewa an bar jama’a su dogara da labaran kafafen sada zumunta maimakon bayani daga hukumomi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fito da bayanai kan harin da Amurka ta kai jihar

Ta bayyana lamarin a matsayin shugabanci mara tausayi da sakaci, musamman a lokacin bukukuwa da jama’a ke bukatar zaman lafiya.

PDP ta bukaci gwamnan Kwara ya gaggauta dawowa daga Abuja, ya ziyarci Offa, ya nuna goyon baya ga mutanen da abin ya shafa.

Ta kuma nemi gwamnan ya yi wa al’ummar Kwara cikakken bayani, tare da hada taron tsaro domin kawar da tsoro da ruɗani.

Jam’iyyar ta jaddada cewa mutanen Offa sun cancanci gaskiya, kariya da shugabanci nagari a irin wannan lokaci mai sarkakiya.

Wuraren da harin Amurka ya shafa

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce hare-haren hadin gwiwa da Amurka sun kai ga manyan sansanonin 'yan kungiyar ISIS a dajin Bauni da ke Tangaza.

Ministan yada labarai na kasa, Mohammed Idirs ya bayyana cewa an yi aikin ne bayan cikakken sahalewar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

Mohammed Idris ya ce burbudin makaman da aka harba ne suka faɗa yankunan Jabo da Offa kuma babu fararen hula da suka rasa rai a sanadiyyar hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.