An Samu Gawar Ma'aikaci a Gidan Gwamnatin Gombe cikin Halin ban Mamaki

An Samu Gawar Ma'aikaci a Gidan Gwamnatin Gombe cikin Halin ban Mamaki

  • An tsinci gawar wani ma’aikacin wucin-gadi da ke aiki a Gidan Gwamnatin Jihar Gombe cikin yanayi mai ɗaga hankali da cike da tambayoyi
  • Wani rahoto ya ce an garzaya da shi zuwa asibiti bayan ganin shi kwance ba tare da yana motsi ba, sai dai daga bisani likitoci sun ce ya rasu
  • ’Yan sanda sun cafke wani mutum da ake zargi da hannu a kisan, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Wani ma’aikacin wucin-gadi da ke aiki a Gidan Gwamnatin Jihar Gombe ya rasa ransa a ranar 26, Disamba, 2025, a wani lamari da ya janyo hankalin jama’a da jami’an tsaro.

Lamarin ya faru ne a cikin harabar Gidan Gwamnatin, inda aka tsinci mamacin kwance ba tare da motsi ba a wani sashe na Taraba House da aka kammala gyaransa kwanan nan.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Gidan gwamnatin jihar Gombe
Kofar shiga gidan gwamnatin jihar Gombe. Hoto: Usman Usman
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa mutuwar ta faru ne a yanayi mai cike da tambayoyi, lamarin da ya sa ’yan sanda suka fara bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

An samu gawa a gidan gwamnatin Gombe

Majiyoyi sun bayyana cewa mamacin, mai suna Malam Umar, wanda aka fi sani da Baba Usama, yana aiki ne a matsayin mai kula da rijiyar burtsatse a sashen gidan gwamnatin da ake kira Taraba House.

A cewar bayanan da aka samu, an gano shi ne da misalin ƙarfe 3:50 na rana, inda aka same shi kwance ba tare da motsi ba.

An ce an daure wuyansa da wandon da yake sanye da shi, yayin da aka samu wani sinadarin maye na gargajiya a bakinsa.

Nan take aka yi gaggawar kai shi Asibitin Kwararru na Gombe, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa bayan an duba shi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fito da bayanai kan harin da Amurka ta kai jihar

Matakin da ’yan sandan Gombe suka dauka

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro suka fara bincike domin gano wadanda ke da hannu a kisan ma'aikacin.

Rahotanni sun nuna cewa da misalin ƙarfe 11:00 na dare, jami’an ’yan sanda karkashin jagorancin DPO na Pantami sun samu nasarar cafke wani da ake zargi.

An ce an kama wanda ake zargin mai suna Shuaibu Adamu ne a maboyarsa da ke unguwar Bagadaza a birnin Gombe.

Majiyoyi sun ce bayan kama shi, ya amsa cewa yana da hannu a aikata laifin, kodayake bincike na ci gaba domin tantance cikakkun dalilai da yadda abin ya faru.

Gwamnan jihar Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: UGC

’Yan sanda sun bayyana cewa za a ci gaba da zurfafa bincike domin tabbatar da gaskiyar ikirarin da aka yi da kuma gano ko akwai wasu da ke da hannu a kisan.

Kokarin tuntubar 'yan sandan Pantami

A ƙoƙarin samun karin bayani daga hukumomin tsaro, wakilinmu ya tuntubi DPO na hedikwatar ’yan Sandan Pantami, Ahmed Umar Sanda, domin jin ta bakinsa.

Kara karanta wannan

An baza 'yan sanda ta ko ina a Maiduguri bayan harin bam a masallaci

Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, bai amsa kiran waya ko saƙon da aka tura masa ba.

Wannan ya sa jama’a ke ci gaba da jiran cikakken bayani daga ’yan sanda kan matakin da aka dauka.

An kama mai garkuwa da mutane a Kwara

A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kwara ta kama wani kasurgumin dan bindiga mai garkuwa da mutane.

An kama dan ta'addan ne bayan ya wallafa wani bidiyonsa a kafar sada zumunta yana nuna makamai da makudan kudi a kwanakin baya.

Rahoton da 'yan sanda suka fitar ya nuna cewa an samu dan ta'addan da tarin makamai da kudi kimanin N500,000 da wasu kayayyaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng